• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Siyasa ba ta haifar da da mai ido ba a Najeriya: tsohon ministan matasa

aksam by aksam
June 7, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
469
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Tsohon ministan matasa da wasanni, Barista Solomon Dalung ya ce shi a fahimtarsa Najeriya ba ta kai mizanin da ake so ba dangane da romon dimokraɗiyya.

“A shekara 25 ɗin nan a gare ni ba ta haifi ɗa mai do ba….An sami komabaya a tattalin arziki na Najeriya domin a 1999 lokacin da aka kawo wannan dimokraɗiyya, canjin dala a lokacin yana ƙasa da naira 10 amma a yau muna maganar kusan naira 1500.” In ji tsohon ministan.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Dangane da ilimi, Dalung ya ce “ba ma za ka taba haɗa ingancin ilimi na wancan lokacin da na yanzu ba.”

Harkar noma da kiwo da zamantakewa da tsohon ministan ya yi magana a kai, ya ce duka komabaya aka samu.

Da aka tambaye shi ko daga wane lokaci al’amura suka taɓarɓare kasancewar shi ma ya kasance a wata gwamnati a baya. Sai ya ce ” tsarin ne ba mai kyau ba. Idan da a ce irin na Birtaniya ne da shugaban ƙasa dole sai ya yi shawara da majalisa kafin yanke hukunci. Amma yau shugaban ƙasa zai yi gaban kansa ya bai wa hukumar alhazai kaza, wannan kaza.”

Halin ‘yan siyasa ya fi na sojoji muni
Solomon Dalung ya ce abin takaici shi ne yadda halayen ƴan siyasa ya yi muni fiye da na sojoji.

“Abin da ‘yan siyasa suke yi ya fi na sojoji muni a yanzu bisa rashin tausayin da suke nunawa da kuma halin matsi da suka jefa ‘yan Najeriya.”

Sai dai kuma ya ce sojojin ne suka lalata al’amarin mulkin dimokraɗiyya a Najeriya.

“Sojoji sun azabtar da ‘yan siyasa sakamakon fadi tashin da burgimarka hankaka da suka yi.”

Daga ƙarshe barista Dalung ya ce abin da ke tayar masa da hankali shi ne irin halin matsin da ƴan Najeriya ke ciki a yanzu.

Share188Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Rikicin sarauta: Yanzu haka wata babbar kotun tarayya na sauraron karar da Aminu Ado ya shigar

Next Post

Wajibi Majalisa Ta Bincike Dalilan Dakatar Da Hakar Mai A Kalmani Bauchi; Dakta Dukawa

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Innovating Game Design: Strategic Lessons from the Chicken vs Zombies Universe

April 21, 2025
Kalli mataki na biyu na mayar da fadar mulkin Nageriya Legas

Kalli mataki na biyu na mayar da fadar mulkin Nageriya Legas

January 27, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media