• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Musa Garba Kwankwaso (BABA), Ya Ce Zai Garzaya Kotu Domin Kalubalantar Hukumomin Yaki Da Cin Hanci Da Rashawar Kasannan

aksam by aksam
August 22, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home SIYASA
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Hassan Umar Gwammaja

Garba Kwankwaso ya bayyana haka ne jim kadan bayan ya amsa gayyatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar (PCACC) ta yi masa a ranar Alhamis tare da lauyoyinsa.

RelatedPosts

Dawo da tallafin man fetur

Anci gaba da rabon tallafin Naira 100,000 duk wata ga matasa 1,300 a Kano ta Arewa

Mataimakin shugaban kasa zai jagoranci tawaga zuwa Jamhuriyyar Benin

Daily Trust ta ruwaito cewa Hukumar PCACC ta shirya wata ganawa da Manajan Daraktan Kamfanin Magunguna na Novomed, Musa Garba Kwankwaso, kan badakalar kwangilar samar da magunguna ta miliyoyin Naira.

Wasikar mai dauke da sa hannun shugaban sashin ayyuka na hukumar CSP Salisu Saleh a madadin shugaban hukumar ta bayyana cewa, “Hukumar tana binciken laifin karya sashe na 31 da 33 na dokar sayo kayan gwamnati da kuma tsarin kula da harkokin kudi dangane da kwangilar da ma’aikatar ta bayar ga Kananan Hukumomin Jihar Kano ga Kamfanin ku (Novomed Pharmaceuticals) domin samar da magunguna ga Kananan Hukumomi 44.”

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta sami umarnin hana cire kudi a asusun Novomed Pharmaceuticals, inda ta toshe sama da Naira miliyan 160 yayin da take kokarin kwato sauran kudaden.

Da yake magana, lauyan Kwankwaso, Barista Okechukwu Nwaeze, ya ce, “Hukumomi uku da suka hadar da ICPC, EFCC da PCACC suna bincike akan mutum daya kan laifi iri daya, Kuma dukkaninsu sun mika masa goron gayyata bana jin kundin tsarin mulkinmu ya yarda da hakan.

“Mun kai wannan magana gaban kotu, domin ta warware matsalar domin batun akwai rudarwa a cikin sa.

“Mun yanke shawarar tafiya kotu domin warware dambarwar ta yadda hukumomi uku ba za su iya bincike akan mutum daya kuma akan laifin daya.”

Idan za a iya tunawa Aksam Media ta rawaito Dan Bello ne dai ya fara fallasa cewa kananan hukumomin Kano suna baiwa kamfanin Novomed kwangilar Naira miliyan 10 wannensu domin sayo Magunguna, a cikin wani bidiyo da ya saki, sai dai gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce bai sance da cewa ana ba da kwangilar ba, Sannan kuma ya baiwa hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta jihar ta gudanar da bincike tare da mika masa rahoton binciken domin daukar matakin da ya dace.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Babban Mai Shari’a Na Kasa Olukayode Ariwoola Ya Yi Ritaya A Matsayin Alkalan Alkalan Najeriya Bayan Cika Shekarun Aiki Na Shekara 70

Next Post

Sarkin Kano Na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero Ya Bar Jihar Kano Zuwa Abuja A Karon Farko Tun Bayan Dawowarsa Jihar A Watan Mayu

aksam

aksam

RelatedPosts

Atiku Ya Nemi Tinibu Ya Fadi Inda Ya Saka Tiriliyan 30 na Tallafi Mai Da Ya Cire.
SIYASA

Dawo da tallafin man fetur

by Khadija Maitaya
August 26, 2026
Anci gaba da rabon tallafin Naira 100,000 duk wata ga matasa 1,300 a Kano ta Arewa
SIYASA

Anci gaba da rabon tallafin Naira 100,000 duk wata ga matasa 1,300 a Kano ta Arewa

by Khadija Maitaya
July 28, 2026
Mataimakin shugaban kasa zai jagoranci tawaga zuwa Jamhuriyyar Benin
SIYASA

Mataimakin shugaban kasa zai jagoranci tawaga zuwa Jamhuriyyar Benin

by Khadija Maitaya
July 23, 2026
Daukar DanKwankwaso Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Gwamnan Kano A NDC Ya Jaho Ce-ce-ku-ce
SIYASA

Daukar DanKwankwaso Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Gwamnan Kano A NDC Ya Jaho Ce-ce-ku-ce

by aksam
June 16, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Natanyahu ya nemi Amurka ta shiga yaƙin da ƙasar sa ke yi da Iran

Natanyahu ya nemi Amurka ta shiga yaƙin da ƙasar sa ke yi da Iran

June 15, 2025
Yau ce Ranar Radiyo Ta Duniya

Yau ce Ranar Radiyo Ta Duniya

February 13, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media