Hukumar Hisbah ta jihar Kano tace ta sami nasarar sake kama shahararriyar jarumar TikTok mai suna Murja Ibrahim Kunya.
Hukumar Hisbah ce da kanta ta tabbatar da hakan, Inda tace sun kama Murja Kunya ne sakamakon ci gaba da tayi da yin abubuwan rashin da’a, da suka sabawa koyarwar addinin Musulinci.
Idan za’a iya tunawa a baya hukumar ta gayyaci murja da sauran Taurarin TikTok don yi mata nasiha tare da lura da irin abubuwan da ta ke aikata wa a shafukan sada zumunta amma ba ta sauya ba, hakan ne ya sanya hukumar ta kama ta.
Jarumar dai ta shahara, wajen furta kalaman batsa masu nuna tsagwaron rashin tarbiya da kuma sanya sutura da ta saba wa addinin musulinci da al’adar Hausawa tare da kwaikwayon wasu al’adu na daban.
Tun a bayan dai jama’a da dama ke ganin baikon hukumar Hisbar na kin kama Murja Kunya sakamakon yadda ta shafa wa idon ta da toka, ta ke shuka rashin mutunci a shafukan sada zumunta, iya son ranta.













Hmmm Allah yakyauta Amma yakamata wannan shafun na tiktok arufeshi ajahar kano tunda addinin mubaibada damar yada badalaba kosu dasuke yan jaharkano idan basudaura abunda baidaceba to wasu zasudaura yan wasu jahohin daban kuma yan jahar kanon idan sunhau aizasu gani