• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Matashi Dan Kano Ya Yanke Gaban Sa

aksam by aksam
May 12, 2026
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Hassan Umar Gwammaja

Wani matashi ɗan asalin jihar Kano mai suna Sani, daga unguwar Tukuntawa da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, ya shiga wani mawuyacin hali a ƙasar Libya bayan da ya yanke gaban sa sakamakon matsalar ƙwaƙwalwa da ake zargin ya kamu da ita. Kano City Guide

RelatedPosts

Sabon CP na Jihar Sokoto Ya Nemi Goyon Bayan Sarkin Musulmi

Malamai Sun Fito Zanga-zanga A Jihohi, Sun Nemi A Ceto Malamai Da Daliban Da Aka Sace A Oyo

Zuwa Aiki A Makare: Gwamnatin Kano Ta Gargadi Ma’aikata

Rahotanni sun nuna cewa matashin ya tafi ƙasar Libya ne domin neman na kai, sai dai daga bisani ya fara fama da matsalar ƙwaƙwalwa yayin da yake aiki a wata ma’aikata a ƙasar.

A cewarsa, matashin ya fara nuna alamun rashin lafiyar ƙwaƙwalwa tun watannin baya, lamarin da ya jefa abokan aikinsa da sauran ’yan Najeriya da ke tare da shi cikin damuwa.

“Bayan an killace shi ne sai aka ji yana ihu. Da aka duba shi kuma sai aka same shi cikin jini bayan ya yanke gaban sa,” in ji shi.

Ya kara da cewa lokacin da suka isa wajen, sun tarar da matashin cikin mawuyacin hali, inda ya yi asarar jini mai yawa.

“Da muka duba sai muka gano ya yanke gaban sa, saura kaɗan ya rage bai rabu gaba ɗaya da jikinsa ba. Lamarin ya tayar mana da hankali sosai,” a cewar Fagge.

Ya ce har yanzu ba a gano musabbabin matsalar ƙwaƙwalwar da ta same shi ba, amma kungiyar tasu ta haɗa kuɗi domin kai shi asibiti cikin gaggawa domin ceton rayuwarsa.

A cewarsa, likitoci na shirin yi masa tiyata saboda sashen jikin bai gama yankewa gaba ɗaya ba.

Fagge ya kuma yi korafin cewa tun bayan fara lalacewar lafiyar matashin suka sanar da ofishin jakadancin Najeriya da ke Libya, amma babu wani mataki da aka ɗauka.

Ya ce a yanzu haka matashin na kwance a asibiti yana samun kulawar likitoci, yayin da suke kokarin ganin an dawo da shi Najeriya domin ci gaba da yi masa magani.

“Idan ba a samu taimako daga gwamnati ba, za mu haɗa kuɗi tsakaninmu domin ɗaukar nauyin dawo da shi gida Kano ta jirgi,” in ji shi.Kano City Guide

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Sirrin Tsawon Rai: Me Yasa Wasu Ke Kai Shekara 100?

Next Post

Yadda Wata Mata Ta Banka Wa Mijinta Da Amaryarsa Da ‘Ya’yanta Guda Biyu Wuta A Kano ‎ ‎

aksam

aksam

RelatedPosts

Sabon CP na Jihar Sokoto Ya Nemi Goyon Bayan Sarkin Musulmi
LABARAI

Sabon CP na Jihar Sokoto Ya Nemi Goyon Bayan Sarkin Musulmi

by Khadija Maitaya
June 4, 2026
Malamai Sun Fito Zanga-zanga A Jihohi, Sun Nemi A Ceto Malamai Da Daliban Da Aka Sace A Oyo
LABARAI

Malamai Sun Fito Zanga-zanga A Jihohi, Sun Nemi A Ceto Malamai Da Daliban Da Aka Sace A Oyo

by aksam
June 2, 2026
Gwamna Abba Kabir ya rantsar da alkalai Tara da kadi hudu
LABARAI

Zuwa Aiki A Makare: Gwamnatin Kano Ta Gargadi Ma’aikata

by aksam
June 2, 2026
Majalisar Dokokin Ghana Ta Amince Da Dokar Hana Ayyukan LGBTQ+
LABARAI

Majalisar Dokokin Ghana Ta Amince Da Dokar Hana Ayyukan LGBTQ+

by aksam
June 2, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Gwamnatin kano ta yaba da Shirin AGILE

Gwamnatin kano ta yaba da Shirin AGILE

September 27, 2023
Gwamnatin Jihar Kano ta Rufe Asusun Ma’aikatun ta

Gwamnatin Jihar Kano Ta Saka Ranar 16 Ga Watan Satumba Domin Komawa Makarantar Firamare Da Sakandire Na Zangon Farko Na Shekarar 2024/2025 Ga Dukkan Makarantun Kwana Da Na Firamare Masu Zaman Kansu Dake Jihar

September 12, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Hukumar Tace Fina-finai Ta Kano Ta Dakatar Da Wasu Jaruman Kannywood Biyu

Hukumar Tace Fina-finai Ta Kano Ta Dakatar Da Wasu Jaruman Kannywood Biyu

May 17, 2026
Yadda Wata Mata Ta Banka Wa Mijinta Da Amaryarsa Da ‘Ya’yanta Guda Biyu Wuta A Kano ‎ ‎

Yadda Wata Mata Ta Banka Wa Mijinta Da Amaryarsa Da ‘Ya’yanta Guda Biyu Wuta A Kano ‎ ‎

May 13, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media