Daga Hassan Umar Gwammaja,
Makarantun kwana a fadin jihar za su koma ranar Litinin 16 ga Satumba, 2024.
Idan dai ba a manta ba, kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya sanar a ranar Asabar 7 ga watan Satumba, dage ranar da za a koma makaranta.
A wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu, ta bukaci iyaye/masu kula da daliban da su lura da sabon ranar da za su ci gaba da aiki domin tabbatar da cikakken bin doka.
Sanarwar ta sake jaddada kudurin gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusif na ganin kowane yaro ya samu ilimi mai inganci.
“Gwamnati na daukar matakai masu kyau wajen samar da ingantaccen yanayin koyo da zai zaburarwa da karfafawa dalibanmu kwarin gwiwa a fannin ilimi,” in ji sanarwar.












