RelatedPosts
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gayyaci Shugaban Hukumar Ilimin Bai ɗaya ta Jihar Kano (SUBEB Kano State) domin yi masa bayani kan zargin rashin gamsuwa da yadda hukumar ta gudanar da aikin ɗaukar ma’aikata na baya-bayan nan.
Wannan mataki na zuwa ne bayan da ‘yan majalisar suka nuna damuwa kan yadda aka ce an gudanar da aikin daukar ma’aikata a hukumar, wanda suka ce akwai buƙatar a sake dubawa domin tabbatar da adalci da bin ƙa’ida.
Da yake gabatar da kudirin nuna rashin gamsuwa a zauren majalisar, dan majalisar jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Danbatta, Hon. Murtala Musa Kore, ya buƙaci majalisar da ta shiga lamarin tare da tabbatar da cewa an sake duba tsarin daukar ma’aikatan da aka yi
Ya bayyana cewa akwai korafe-korafe daga wasu masu neman aiki da ke zargin cewa ba a bi tsarin gaskiya da adalci ba wajen tantance sunayen da aka fitar, lamarin da ya ce ya haifar da damuwa a tsakanin al’umma
Bayan gabatar da kudirin, majalisar ta amince da kiran shugaban SUBEB domin ya bayyana wa ‘yan majalisar yadda aka gudanar da aikin, tare da bayar da cikakken bayani kan tsarin da aka bi wajen daukar ma’aikatan.
Majalisar ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da bin diddigin lamarin domin tabbatar da cewa dukkan matakan gwamnati suna aiki bisa gaskiya, adalci da kuma bin doka.
Ana sa ran cewa bayan zaman sauraron da shugaban SUBEB zai yi a gaban ‘yan majalisar, za a iya daukar matakai na gyara ko tabbatar da sahihancin aikin da aka gudanar.











