Matashi Dan Asalin Karamar Hukumar Bichi Dake Unguwar Takalmawa
Ya Fada Ragar Kwamitin Masallacin Jumaa Na Garin Karfi Tare Da Alummar Garun Karfi Dake Chan Karamar Hukumar Kura.Matashin ana Zarginsa Da Zuwa Masallacin Jumaa Dake Bakin Titi Da Yunkurin Satar Sabbin Takalman Alumma
Mutumin Mai shekaru 25 Maisuna Sani Takalmawa Bichi Ya Tabbatarwa Da Kotun Shariar Musulunci Ta Kura
Ƙarƙashin Jagorancin Mai sharia Malam Ibrahim Isa Usman Cewar Ya Aikata laifin.
Bayan dan sandan kotu Mai gabatar Da Kara P C Saifullahi Nasidi Kura
Ya Karanta Masa Takardar Tuhumar Zargin Aikata Laifin Nan Take Ya Amsa
Ya Kuma Roki Sassauci.
Mai sharia Malam Ibrahim Isa Usman
Ya Kafa Masa Shedun Jin Ikkirari Da Mutun Biyu Mai shariar Kotun Ya Yanke Masa Hukunci Da Wata Daya a Gidan Ajiya Da Gyaran Hali
Ya Kuma Gargade Shi Da
Ya Zama Mutumin Kirki Wato Mutun Nagari
Alkalin Kotun Ya Sanyashi a Hanun Jamiin Gidan Ajiya Da Gyaran Hali
Insifector Awwalu Muhammd Danhasan
Sannan Ya Umarcesh Bayan Ya Kaishi
Ya Tabbatar Ya Sanyashi a Masallacinn Gidan Ajiya Da Gyaran Hali Bisa Kulawar Limamin Masallacin Dan Koya Masa Kan Abun Da Ya Shafi Addinin Musulunci












