DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da iyalansa basu halarci zaman kotun, da aka gudanar ba a wannan rana bisa tuhumarsu da laifin almundahana na biliyoyin naira.
Rashin bayyanar Ganduje a gaban kotun a yau ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin wadanda suke je sauraren karar, yayin da suke kokarin tantance ko rashin bayyanar Ganduje Rashin girmama kotu ne
Sauran wadanda ba su halarci kotun ba sun hada da matarsa, Hafsat Ganduje,
Danta, Umar Ganduje, da wasu mutane 5 da ake zargi .
Sai dai ba a bayyana dalilin da ya sa tsohon gwamnan wanda kuma shi ne shugaban jam’iyya mai mulki na kasa ya kasa bayyana a gaban kotu, amma wasu makusancinsa da ba a bayyana sunansa ba ya bayyana cewa “Dr. Ganduje ba ya kasar.”









