Daga Hassan Umar Gwammaja
A wani bangare na bunkasa harkokin ilimi a Arewacin Najeriya, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Rt Hon Yusuf Dahiru Liman ya biyawa daliban su kimanin 1000 da suka fito daga yankinsa kudadin jarrabawar kammala sakandire Kudadin da suka kai naira miliyan 40
Tun da farko an gudanar da jarrabawar gwajine ga daliban a harabar makarantun sakandiren ‘yan mata dake Barnawa a Karamar Hukumar Kaduna Ta Kudu
Alhaji Bashir Adamu Na Baba shi ne Shugaban Ma’ikatan kakakin Majalisar yace wanna ba sabon abubane a wajan shugaban majalisan ko a shekarar da ta gabata ya biyawa dalibai 500 kudadin jarrabawar NECO
Wasu dagacikin daliban da kabiyawa kudin sun bayyana godiyarsu da Rt. Hon Yusuf Dahiru Liman din











