Gwamnatin tarayya ta sanar da daukar sabon mataki domin wadata a Najeriya da abinci.
Hakan na dauke ne cikin wani sako da mai taimakawa shugaba Bola Tinubu a kan harkokin sadarwa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X.
Ya ce gwamnatin ta yi alkawarin cewa farashin abinci zai karye a cikin watanni masu zuwa.
Onanuga ya wallafa cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sayen motocin noma kirar tarakta kanana guda 2,000.
Mai taimakawa shugaban kasar ya kara da cewa shugaba Tinubu ya kara bayar da umurnin sayen manyan tarakta guda 1,200.
Gwamantin tarayyar ta kara da cewa za a sayo garma da za a rika amfani da su samfura daban-daban.
A dunkule, za a sayo garma kimanin 5,000 domin ganin ayyukan noma sun bunkasa a Najeriya, rahoton Leadership
Bayo Onanuga ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ba da kwangilar aikin ne ga kamfanin harkar noma na MAP.











good news