ADVERTISEMENT
465
SHARES
1.5k
VIEWS

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabeer Yusuf, ya ba da umarnin gaggauta dakatar da Hon. Ibrahim Rab’iu, babban hadimin dake bada rohoto ( SSR ) a ma’aikatan sufuri saboda furta maganganun da basu da ce.

Gwamnan ya kuma bada umarnin a sabunta hadimin da  takardar tuhuma ta aikata laifi  saboda furta kalaman kage na sauya jam’yya  ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ya shafi sauya sheka.

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ne ya gabatar da dakatarwar wanda Kuma tuni ta  ya fara aiki tun jiya Asabar.

Daraktan yada labaran fadar gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a wani sako da ya fitar ya  bayyana cewa, gwamna ya ja kunnen masu rike da mukaman siyasa a jihar Kano akan furta kalaman da ba aminta da su ba.

Jadawalin Bayanin Bayan Taron Gwamnonin Arewa Ya yi dai dai da manufar Gwamna Dan-modi

Sunusi ya kuma bayyana cewa, gwamnatin Kano ta nesanta kanta da kalaman, tare da kwatanta maganganun hadimin da aka dakatar a matsayin kirkira ce ta kashin kansa.

Gwamnati tana sake tunatar da dukkan al’umma cewa, kwamishanan yada labarai da kuma kula da ayyukan cikin gida, kwamred Ibrahim Waiya ne kadai yake da izinin magana da yawun gwamnati, Sannan Sunusi Bature, ke  magana ne da yawun gwamna..

Hukumar JAMB ta dauki hanyar rusa ilmi a Arewa – Mai sharhi

Duk mai rike da mukamin siyasa, dole ne ya nemi izinin amincewa kafin ya bayyana kalamansa ga jama’a, dangane da abun da ya shafi gwamnati da mahimmancin al’ummanta ko yanke shawara akan siyasa.


 

ADVERTISEMENT

RelatedPosts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

ADVERTISEMENT

Trending.