Daga Hassan Umar Gwammaja
Cikin wani jawabi da ya yi wa manema labarai a gidan gwamnatin jihar ranar Juma’a, Mista Eno ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntuɓar abokan shawararsa.
“Kan haka ne na ɗauki matakin fita daga PDP tare da komawa jam’iyyar APC”, kamar yadda gwamnan ya bayyana.
Gwamnan ya ce ya koma APC ne domin ƙarfafa jam’iyyar.
“Ba mu shiga jam’iyyar daga ɓangaren masu gazawa ba, mun shiga ne domin ƙarfafa jam’iyyar,” in ji shi.
Mista Eno ya ce ya koma APC ne domin taimaka wa sauye-sauyen tattalin arziki na shugaban Najeriya Bola Tinubu.
Ficewar Eno daga PDP na zuwa ne ƙasa da wata biyu bayan gwamnan Delta Sheriff Oborevwori, ya fice daga jam’iyyar adawar ta PDP zuwa APC











