• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Binciken masana ya gano ƙasar Rasha na faɗaɗa ikon sojinta a Afirka

aksam by aksam
June 10, 2025
Reading Time: 3 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Rasha na faɗaɗa ikon sojinta a Afirka: rahoto
Rasha ta sake fasalin ayyukan sojinta a Afirka, inda Kremlin ta karɓi iko mafi girma ta hanyar jibge sojojinta a Afirka.

Rasha na ƙara faɗaɗa ikon sojinta a nahiyar Afirka, inda take isar da manyan makamai zuwa yankin kudu da hamadar sahara da ake fama da rikici, yankin da dakarun da ke ƙarƙashin ikon Kremlin ke daɗa bazuwa.

RelatedPosts

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

La’akari da takunkuman da kasashen Yamma suka ƙaƙaba mata, Moscow na amfani da jiragen dakon kaya domin aike wa da tankokin yaki, da motoci masu sulke, da manya-manyan bindigogi da sauran na’urori masu daraja zuwa Yammacin Afirka, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya gano.

Kafar AP dai ta dogaro da hotunan tauraron ɗan adam da sadrwa ta rediyo, inda ta bibiyi ayarin jiragen dakon kaya masu ɗauke da tutar Rasha, yayin da suka yi tafiyar kusan wata guda daga tekun Baltic.

Jiragen ruwan na dauke da motocin igwa da wasu na’urori da sauran kayayyakin aikin soji, a cewar jami’an soji a nahiyar Turai da ke sa ido kan lamarin.

Rundunar sojin wanda ta kwashe shekaru biyu a Afirka, wacce ke da alaƙa da wani reshe na ɓoye na sojojin Rasha, ta samu ƙarfi ne a daidai lokacin da sojojin Amurka da na Turai ke janyewa daga yankin, waɗanda kasashen yankin Kudu da Hamadar Sahara suka tilasta wa barin yankin kana suka koma ga Rasha domin samun tsaro.

“Muna da niyyar faɗaɗa haɗin gwiwarmu da ƙasashen Afirka a dukkan fannoni, tare da mai da hankali kan haɗin gwiwar tattalin arziki da zuba jari,”a cewar kakakin Kremlin Dmitry Peskov, yana mai ƙari da cewa “wannan haɗin gwiwar ya haɗa da wasu sassa masu mahimmanci da ke da alaƙa da tsaro da kare kai.’’

Ga Mali

Daga tashar jiragen ruwa, ana jigilar makaman Rasha zuwa Mali.

Jirgin ruwan Rasha na yankin Baltic mai nauyin tan 8,800 da na Patria mai nauyin ton 5,800 na daga cikin ɗaruruwan jiragen ruwa da Ƙasashen Yamma suka sanya wa takunkumi domin kakkaɓe tasirin yaƙin Rasha da Ukraine.

A ƙarshen watan Mayu ne jiragen suka sauka tare da sauke kayayyakin da suka ɗauko a birnin Conakry na kasar Guinea, kamar yadda hotunan tauraron ɗan adam na AP suka nuna.

Kazalika, sauran wasu jiragen ruwan sun sauke kayayyaki a tashar ruwan a watan Janairu, inda suka kai tankokin yaƙi da motoci masu sulke da sauran kayan aikin da aka yi jigilar su ta ƙasa zuwa maƙwabciyar ƙasar Mali, kamar yadda jami’an sojan Turai da wani faifan bidiyo na kasar Mali suka nuna ayarin motocin da suka isa wurin.

Kafar AP ta tabbatar da bidiyon a wani shafin yanar gizo, inda motocin suka karkata zuwa babban titin RN5 da ke shiga Bamako, babban birnin ƙasar Mali.

Bayan isar kayayyakin a baya bayan nan a birnin Conakry, an sake ganin wasu manyan motoci ɗauke da motoci masu sulke na Rasha, da igwa-igwa da sauran kayayyakin aiki a kan hanyar da ke zuwa Mali.

Kafar yaɗa labaran Mali ORTM ta tabbatar da cewa sojojin da ke yankin Yammacin Afirka sun kai wasu sabbin kayayyakin aikin soji.

Binciken AP kan bidiyo da hotunan da mawallafin na Mali ya ɗauka a daidai wurin da aka yi jigilar kayayyakin a watan Janairu ya gano tarin kayayyakin da aka samar daga Rasha, waɗanda suka haɗa da bindigogi kirar mm 152 da sauran ƙananan bindigogi.

Kazalika AP ta gano wata mota mai sulke ƙirar BTR-80 wacce ke haɗe da na’urar da ke ɗauke sabis, da kuma motocin sulke na Spartak da wasu wadanda ke ɗauke bindigogi da dai sauransu.

Jirgin ya kuma haɗa da aƙalla kananan jiragen ruwa guda biyu, ɗaya ɗauke da fentin tutar Rasha, da kuma manyan motocin dakon kaya, wasu masu ɗauke da tambarin “inflammable” da harshen Rashanci a dukkan gefensu.

Jami’an sojan da suka zanta da AP sun ce sun yi imanin cewa Rasha ta ware manyan kayayyakin aiki ne, musamman bindigogi da kuma na’urorin da ke dauke sabis ga dakarunta na Afirka ba sojojin Mali ba.

Haka kuma alamu sun yi nuni da cewa, an bai wa rundunar sojojin da ke Afirka ƙarfi ta sama, inda tauraron dan adam ya hango akalla jirgin yakin Su-24 guda ɗaya a sansanin sojin saman Bamako a watannin baya-bayan nan.

Dakarun Faransa sun tallafa wa ayyukan yaƙi da ta’addanci a Mali da makwabciyarta Burkina Faso da Nijar. Amma Faransa ta janye sojojinta bayan juyin mulkin da aka yi a Mali a shekarar 2020 da 2021, da Burkina Faso a 2022 da kuma a Nijar a 2023. yayin da sojojin hayar Rasha suka cike giɓin.

Ƙungiyar Wagner, wadda ta yi fice, ta jibge dakarunta a Sudan a 2017 kana ta faɗaɗa ayyukanta zuwa wasu ƙasashen Afirka, inda a mafi yawan lokuta ta ke musayarsu da albarkatun ƙasa.

Daga cikin ƙasashe 33 na Afirka da dakarun hayan sojan Rasha ke aiki a cikinsu, mafi yawancin su sojojin Wagner ne ke sarrafa su, a cewar wani bincike da gwamnatin Amurka ta ɗauki nauyin yi na RAND.

Sai dai bayan da sojojin Wagner suka yi tawaye a Rasha a shekarar 2023 da kuma mutuwar shugabansu, Yevgeny Prigozhin bayan watanni biyu a wani hatsarin jirgin sama, Mo

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Shugaban kasar China ya gana da takwaransa na Koriya ta kudu

Next Post

Kwamishinan Jinkai Da Walwallar Jama’a Comred Markus Yunana Barda Ya Aika Da Sakon Barka Da Sallah Ga Gwamna Uba Sani, Mai Martaba Sarkin Jama’a Da Kuma Sauran Al’umma Musulmi

aksam

aksam

RelatedPosts

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala
LABARAI

Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala

by aksam
April 17, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID
Uncategorized

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

by aksam
April 17, 2026
Araqchi Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matsaya Ka
Uncategorized

Araqchi Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matsaya Ka

by aksam
April 11, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Rahoton yadda bom ya tashi da wasu a jihar Borno

Rahoton yadda bom ya tashi da wasu a jihar Borno

January 28, 2024
Mako mai zuwa na iya girgiza kasuwannin duniya na Crypto baki ɗaya.

Mako mai zuwa na iya girgiza kasuwannin duniya na Crypto baki ɗaya.

January 18, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media