• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Baya ga kayan abinci, kasar Russia ta aike da tallafin motoci makare da makamai ga kasar Niger

aksam by aksam
April 13, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Gwamnatin rikon kwaryar jamhuriyar Nijar ta sanar da isowar wasu makamai da na’urorin kare sararin samaniyar da tace sun shigo ne albarkacin huldar ayyukan sojan dake tsakanin Nijar din da Russia.

Tashar talbijan RTN mallakar gwamnati ta gwada wani jirgin da ta ayyana a matsayin wanda ke dauke da lodin makaman da suka iso birnin Yamai tare da sojojin Rasha kimanin 100 da za su yi aikin girka wadanan makamai su kuma bai wa takwarorinsu na kasar horo akan yadda za su yi amfani da su.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Jirgin dakon kaya samfarin ILYUSHIN 76 ne ya sauka filin jirgin saman Yamai a cikin daren Laraba zuwa wayewar Alhamis dauke da makaman kare kai daga hare-haren sama hade da wasu na’urorin kariyar sararin samaniya kamar yadda ake gani a wani rahoton da gidan talbijan mallakar gwamnatin Nijar ya watsa.

Wannan wani bangare ne na sabuwar huldar da hukumomin mulkin soja suka kulla da gwamnatin Vladimir Putin a ci gaba da laluben hanyoyin magance matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta. Masani a kan lamuran yankin sahel Dr. Seidik Abba na cewa bai yi mamakin wannan yunkuri na Rasha ba.

Wasu sojojin gwamnatin Rashar a kalla 100 ne aka bayyana cewa sun biyo wadanan kayayyaki da za su jagoranci ayyukan girkawa sannan zasu horar da takwarorinsu na kasar a game da yadda zasu yi amfani da su kamar yadda wani kakakin tawwagar rashawan ya jaddada.

Jigo a kungiyar Front Patriotique ta ‘yan goyon bayan hukumomin CNSP Bana Ibrahim na mai alfahari da abinda ya kira sabuwar tafiya.

Sai dai wani dan fafutika Amadou Roufai Laouan Salao na gamayyar COADDE na da shakku kan tasirin wannan hulda tsakanin Rasha da Nijar.

Ayyukan ashan da ake zargin sojan hayar Rasha a kasashen da kamfanin Wagner ke da kwangila abu ne da ya kamata ya zame wa Nijar manuniya inji Souley Oumarou shugaban kungiyar FCR.

Gwamnatin rikon kwaryar Jamhuriyar Nijar ta sanar da isowar wasu makamai da tace sun shigo ne albarkacin huldar tsakanin kasar da Russia.

Gwamnatin rikon kwaryar Jamhuriyar Nijar ta sanar da isowar wasu makamai da tace sun shigo ne albarkacin huldar tsakanin kasar da Russia.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Gwamnatin Kano Ta Yi Alkawarin Ci Gaba Da Ciyar Da Daliban Makarantun Firamaren Jihar

Next Post

Yadda kananan masana’antu ke koka wa da karin kudin wutar lantarki

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Amurka ta yi Barazanar Kai Hari Kan Ƙasar Da Ta Samu Tana Temakawa Iran

Amurka ta yi Barazanar Kai Hari Kan Ƙasar Da Ta Samu Tana Temakawa Iran

August 20, 2026
Kamfanin Sin Ya Shiga Kasuwar Siminti ta Najeriya Ta Hanyar Siyan Lafarge Africa Kan Dala Biliyan 1

Kamfanin Sin Ya Shiga Kasuwar Siminti ta Najeriya Ta Hanyar Siyan Lafarge Africa Kan Dala Biliyan 1

July 10, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media