• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

An Zargi Wasu Sarakunan Jihar Nasarawa Da Yunkurin Kwace Filayen Talakawa

aksam by aksam
May 12, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
472
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

Daga Hassan Umar Gwammaja

Al’ummar Garin Kaibo Mada dake cikin Karamar Hukumar Keffi ta Jihar Nasarawa, sun zargi Sarakunan Bagaji da Masarautar Keffi da yunkurin kwace filaye da gonakin da suka ce sun gada a wurin iyaye da kakanni.

Hakan ce ta sanya suka fito mazan su da matan su domin gudanar da zanga-zangar lumana a titunan garin domin bayyana rashin jin dadinsu, inda suka yi zagaye dauke da kwalaye da ganye suna rera wakokin neman daukin Gwamnatin Jihar Nasarawa.

A cewar daya daga cikin masu zanga-zangar, Malam Salihu Musa, “Wannan filinmu ne da muka gada daga iyayenmu amma yanzu ana yunkurin kwace shi ba tare da wani dalili ba, adan haka muna kira ga Gwamna Injiniya Abdullahi Sule da ya sa baki cikin lamarin domin kare hakkokinmu”.

Ita ma wata dattijuwa me suna Hajiya Zainab Ibrahim, ta bayyana matuƙar damuwarta inda ta ce, “Idan aka kwace gonakinmu, to da me za mu ciyar da ‘ya’yanmu? Wannan ba adalci bane, kuma ba za mu yarda ba har sai mun ga gwamnati ta dauki mataki”.

Sun kara da cewa filayen da ake kokarin kwacewa su ne ginshikin rayuwarsu, la’akari da sune wuraren noman abincin su da kuma samun kudin shiga.

Mafari kenan da suka bukaci Gwamnatin Jihar Nasarawa da Hukumar Kula da Filaye da su dakatar da duk wani yunkuri na kwace filayen, har sai an gudanar da cikakken bincike tare da baiwa al’umma damar kare kansu.

Yayin da manema labarai suka isa Fadar Masarautar Keffi domin Jin ta bakin Mai Martaba Sarkin Keffi Dakta Cindo Yamusa, ya aiko Sakataren wucin gadi na Masarautar Malam Yakubu, ya sanar da ‘yan jaridun cewa, yana kan hanyarsa ta zuwa ta’aziyya a garin Nasarawa amma da zarar ya shirya zai kira su domin mayar da martani kan wannan zargi.

Share189Tweet118SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Tinubu swears in new INEC

Next Post

Gwamnan Kano Abba Kabeer Yusuf Ya Raba Kayayyakin Harkokin Ilimi Ga Makarantun Jihar

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan
LABARAI

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

by aksam
May 4, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano
LABARAI

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A  Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga  Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC
LABARAI

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC

by aksam
May 3, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Καζίνο live streaming στο powbet casino

April 22, 2025
Sabon Mai Baiwa Gwamnan Kano Shawara Kan Ayyuka, Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure Ya Rasu, Kwana Daya Da Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Rantsar Da Shi a Gidan Gwamnati.

Sabon Mai Baiwa Gwamnan Kano Shawara Kan Ayyuka, Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure Ya Rasu, Kwana Daya Da Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Rantsar Da Shi a Gidan Gwamnati.

January 8, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media