• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

An Rotsa Babura 601 A Abuja

aksam by aksam
April 30, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
469
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

 

Daga Hassan Umar Gwammaja

A ci gaba da kokarin dakile amfani da Babura a Sassan Babban Birnin Tarayya Abuja da ke fama da cunkoso da rashin tsaro, Hukumar gudanarwar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta lalata babura guda 601 da aka kama bisa karya dokar hana zirga-zirgar su.

‎Lalata wadannan Babura ya gudana ne ranar Talata karkashin kulawar Hukumar Kula da Harkokin Motoci da Zirga-zirga (DRTS), a karkashin jagorancin Ministan Abuja, Nyesom Wike. Wannan mataki ya biyo bayan aiwatar da dokar da ke hana amfani da babura a wasu yankuna na birnin, wanda aka fara tun 1 ga Janairu, 2023.

 

Sakataren harkokin sufuri na FCTA, Dakta Elechi Chinedum, ya bayyana cewa wannan aiki yana da nasaba da doka da gwamnatin da ta gabata karkashin tsohon Minista, Mohammed Bello, ta shimfida domin kiyaye doka da oda a birnin.

”Dokar ta kayyade wuraren da ba a amince a rika amfani da babura ba, kuma abin da muka yi yau wata hanya ce ta tabbatar da cikar wannan doka,” in ji Dakta Chinedum.

A nasa jawabin, shugaban DRTS, Dakta Abdulateef Bello, ya bayyana cewa haramcin babura a babban birnin ba sabon abu ba ne, domin tun daga shekarar 2006 aka fara daukar matakin. Ya ce babura suna haddasa cunkoso, hadurra da kuma taimakawa aikata laifuka.

‎”Wannan aiki wata hanya ce ta kara tabbatar da haramcin babura a cikin birnin tarayya. Muna gargadin masu zuba jari a harkar babura da su dakatar da hakan, domin gwamnati za ta ci gaba da kwace su tare da lalata su kamar yadda kotu ta bayar da umarni,” in ji shi.

‎Shi ma jami’in ‘yan sanda mai kula da ayyuka a rundunar FCT, ACP Mode Magawata, ya bayyana damuwa kan yadda ake amfani da babura wajen aikata laifuka kamar fashi da makami da kuma satar muta

 

‎”Minista ya bada umarni cewa babu babura a yankunan da aka haramta, kuma mu a hukumance muna tabbatar da bin wannan umarni,” in ji ACP Maga

‎Wannan mataki na kara nuna kudurin gwamnatin tarayya na tabbatar da tsaro da daidaito a harkokin zirga-zirga a Babban Birnin Tarayya.

 

Share188Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

‎Kotun Soji A Najeriya Ta Yanke Wa Wani Soja Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Next Post

Fadar Shugaban Najeriya Ta Musanta Labarin Sauke Ministocin Kasar Uku

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Jawabin Tinubu ya ja hankalin shugabannin Africa su tausaya wa al’ummar su

Shugaban Bola Ahmad Tinubu Zai Yi Wa ‘Yan ƙasa Jawabi Gobe

August 3, 2024
Sanatoci sun yi martani kan rahotan karbar tallafin kayan abinci da zasu rabawa talakawa

Sanatocin Arewacin Najeriya 12 Da Suka Gaza Gabatar Da Ƙudiri A Watanni 15

October 4, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media