• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Karuwar Yawan Satar Dalibai A Jami’o’in Najeriya; ‘Yan Arewa Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Lumana

aksam by aksam
December 11, 2023
Reading Time: 2 mins read
0
Home TSARO
ADVERTISEMENT
470
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA

Daruruwan dalibai ne suka yi dandazo a Kano a yau Litinin don nuna adawa da yadda ake ci gaba da yin garkuwa da dalibai mata a manyan makarantun Arewacin Najeriya.

RelatedPosts

IGP Ya Umarci CPs Su Yi Bincike Kan Makamai da Harsasai

Rundunar Ƴansandan Nijeriya Ta Kama Wasu Matasa Biyu; Bisa Zarginsu Da Yin Damfara Da Sunan Su Aljannune

Rundunar ‘Yan Sanda Reshin Jihar Gombe Ta Dawo Da Dokar Hana Zirga Zirgar Babura A Jihar

Daliban da suka yi tattaki a unguwar Rijiyar Zaki da ke cikin birnin Kano, sun bukaci a gaggauta ceto dalibai mata da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya ta Gusau wato FUGUS kimanin watanni uku da suka gabata, da kuma wasu da aka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-ma,a jihar Katsina wato FUDMA da sauransur na Jami’ar Jihar Nasarawa dake Keffi.

Kimanin dalibai mata 24 na FUGUS, da kuma dalibai mata hudu na FUDMA da ‘yan bindiga suka kama sama da watanni uku da suka gabata, har yanzu suna hannunsu kamar yanda Jaridar Daily Post ta ruwaito

Sai dai a ranar Lahadin da ta gabata an sako wasu dalibai bakwai na Jami’ar Tarayya da ke Lafia, FULAFIA, Jihar Nasarawa, wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su kwanaki hudu da suka gabata.

Amma har yanzu dalibai hudu da aka kama daga jami’ar jihar Nasarawa watannin baya suna hannunsu.

An gudanar da zanga-zangar ne a karkashin tutar ‘Arewa Mufarka’ ma’ana ‘Yan Arewa mu farka.

Da yake zantawa da manema labarai jagoran zanga-zangar Sharfuddeen Bature, ya ce: “Mun dade muna kan lamarin. Yau kwana tamanin kenan da sace mutanen. Muna da ministocin tsaro a yankinmu jihar Jigawa da jihar Zamfara. Muna da mai ba da shawara kan harkokin tsaro, NSA, daga yankin mu (Jihar Adamawa).

“Muna bukatar dawowar wadannan ‘yan matan. Iyayen su suna cikin mawuyacin hali. Ba za mu daina yin haka ba har sai sun dawo da ‘yan matanmu”.

Masu zanga-zangar sun kuma yi Allah wadai da kisan kiyashin da jiragen yakin sojin Najeriya suka yi a baya-bayan nan sama da mutane 127 a kauyin Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Share188Tweet118SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Hukumar EFCC Na Tuhumar Wasu Ma’aurata Da Aikata Damfarar; Naira Miliyan 410.5

Next Post

Zamu ci gaba da bibiya har sai an yi adalci ga mutanen da harin bomb ya rutsa da su a Tudun Biri: Sarkin Musulmai

aksam

aksam

RelatedPosts

IGP Ya Umarci CPs Su Yi Bincike Kan Makamai da Harsasai
TSARO

IGP Ya Umarci CPs Su Yi Bincike Kan Makamai da Harsasai

by Khadija Maitaya
May 5, 2026
Rundunar Ƴansandan Nijeriya Ta Kama Wasu  Matasa Biyu;  Bisa Zarginsu Da Yin  Damfara Da Sunan Su Aljannune
TSARO

Rundunar Ƴansandan Nijeriya Ta Kama Wasu Matasa Biyu; Bisa Zarginsu Da Yin Damfara Da Sunan Su Aljannune

by aksam
April 16, 2026
Rundunar  ‘Yan Sanda  Reshin Jihar Gombe Ta Dawo Da Dokar Hana Zirga Zirgar Babura A Jihar
TSARO

Rundunar ‘Yan Sanda Reshin Jihar Gombe Ta Dawo Da Dokar Hana Zirga Zirgar Babura A Jihar

by aksam
April 2, 2026
DSS Sun Kubutar Da Sakataren Karamar Hukumar Da Aka Yi Garkuwa Da Shi A Kano
TSARO

DSS Sun Kubutar Da Sakataren Karamar Hukumar Da Aka Yi Garkuwa Da Shi A Kano

by aksam
March 25, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Yau Kimanin Shekara Goma Cif Na Kwashe A Duniya Batar Da Mahaifiyata ba

Yau Ce Ranar Uwa Ta Duniya, Mene ne Abin Da Kuke Yawan Tunawa Da Shi Idan Aka Ambaci “UWA”

May 12, 2024
Mako mai zuwa na iya girgiza kasuwannin duniya na Crypto baki ɗaya.

Mako mai zuwa na iya girgiza kasuwannin duniya na Crypto baki ɗaya.

January 18, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media