DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
A cewar mataimakin shugaban kasa Sen. Kashim Shettima a lokacin da ya kawo ziyarar ta’aziyar jajintawa wadanda da harin ya shafa a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Kaduna wato Barau Dikko dake birnin Kaduna, ya kuma tabbatar da cewa za a hukunta duk mutumin da aka samu da hannu a harin.
Ya kuma alƙawarta cewa gwamnatin tarayya za ta tallafa wa waɗanda suka jikkata a harin.
Ya ce gwamnatin ƙasar a shirye take wajen kawar da ayyukan ta’addanci da fashin daji a yankin arewaci da sauran sassan ƙasar.












