Ƙungiyar kasuwar Singa ta ƙasa reshen Jihar Kano(AMATA)ta bayana cewa,inganta biyan kuɗaɗen leburori kasuwar shine Na farko da Za ta fara sanyawa a gaba da zarar ta kama aiki gadan gadan na Shugabancin kasuwar.
Zababben Shugaban ƙungiyar kasuwar Alh. Musa Nabanki ne ya tabbatar. da Hakan a lokacin da. Yake zantawa da manema labarai a ofishin ƙungiyar kasuwar, Jim kadan bāyyana kammala rantsar Sabon shugabancin ƙungiyar .
Musa Nabanki yace, wannan Sabon shugabancin Yana da managartan tsare tsare da su tallafawa Al’ummar kasuwar Singa yadda ya kamata ta fannoni da dama, musamman leburori.
Shugaban yace, shugabancinsa Zai Yi duk maiyiyuwa wajen Samar da tsaron dukiyoyin al’umma kula da tsaftar kasuwa yadda ya kamata da kawo Dai daito tsakanin ƴankasuwa da abokanan huldarsu ta hanyar kare haƙƙin Mai siye da Mai siyarwa.
Musa Nabanki ya jaddada haɗa kai da Dattawan wannan kasuwa ta ganin an samu albarka da karbar shawarwari Daga garesu ta yadda Za su tallafawa Al’ummar kasuwar Singa,inda kuma yace, Shugabancinsa ba Zai Laminci cin zarafin Wani ba Ko zalintarsa.
Ya kuma bāyyana cewa, Ƙungiyar Za ta haɗa hannu da Gwamnatoci a matakai daban-daban domin samun damar cimmanasarar da ake da buƙata, musamman wajen Samarwa ƴankasuwa tallafi jarin da Za su inganta kasuwancinsu.
Sabon shugabancin ƙungiyar kasuwar ya sha alwashin nemowa Ƴankasuwar hakkokinsu Daga Kano har sauran jihohin Najeriya Na kudu da Arewacin ƙasa domin nuna musu kulawa sakamakon,nauyin da Allah ya dora musu na Shugabancin al’ummar kasuwar Singa.
Shugaban ƙungiyar kasuwar ya yabawa Ma’aikatar kasuwanci da ciniki ta Jihar Kano ƙarƙashin Jagorancin Abas Sani Abas bisa yadda ta shirya Sahin zaɓe da sauran ma’aikatan Ma’aikatar kasuwanci da Jami’an tsaro da yanjaridu,bisa nuna jajircewarsu wajen gudanar ayyukansu cikin kwarewa.
Yace,kwamatin shirya zaɓen ƙungiyar kasuwar ya taka mahimmiyar bisa baiwa al’ummar kasuwar Wanda suka zaba domin samun Dai daito tsakanin Ko wanne ɓangaren Dantakara da Kuma aiwatar da komai a gaban kowa.
Alh Musa Nabanki ya yabawa al’ummar kasuwar Singa,bisa yadda suka jajirce wajen zabarsa a matsayin Shugaban da Zai Shugabancesu,inda ya sha alwashin kawo ayyukan da su ciyar da kasuwar Singa gaba.
Ibrahim Sani Gama pyramid.











