DSS TA GARGADI KAN SHIRIN KAI HARE-HARE WURAREN IBADA
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS, ta gargadi shugabannin addinin Musulunci da Kiristanci a Jihar Osun, kan zargin wani shirin ’yan ta’adda na kai hare-hare a wuraren ibada da kuma tarukan jama’a.
DSS ta bukaci shugabannin addinan da su kara daukar matakan tsaro domin kare rayukan masu ibada.
Daga cikin matakan da hukumar ta ba da shawara akwai hana motoci yin fakin a kusa da masallatai da coci-coci yayin gudanar da ibada, tare da kara tsaron wuraren ibadar.
Hukumar ta ce ana zargin ’yan ta’addan da shirin yada rashin tsaro a yankin Kudu maso Yamma, domin haifar da fargaba da firgici a tsakanin jama’a.
DSS ta kuma yi gargadin cewa ana iya amfani da irin wannan yunkuri wajen kawo cikas ga zaman lafiya da kuma shirye-shiryen gudanar da babban zaben shekarar dubu biyu da ashirin da bakwai.
Hukumar ta bukaci jama’a da su kasance cikin taka-tsan-tsan, tare da kai rahoton duk wani abu ko mutum da ake zargi ga jami’an tsaro.










