NAWOJ Ta Jajantawa Ma’aikatan Pyramid FM Kano Kan Harin ‘Yan Daba
Ƙungiyar Mata ‘Yan Jarida ta Ƙasa, NAWOJ, reshen Jihar Kano, ta kai ziyarar jajantawa ga shugabannin gidan Rediyon Najeriya Pyramid FM Kano, bisa harin da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai wa wasu daga cikin ma’aikatan gidan rediyon, tare da farfasa gilasan motar gidan jim kaɗan bayan kammala taron jam’iyyar APC a jihar.
Shugabar ƙungiyar NAWOJ reshen Jihar Kano, Hajiya Bahijja Malam Kabara, ta ce sun kai ziyarar ne domin jajantawa ma’aikatan gidan rediyon tare da bayyana rashin jin daɗinsu bisa wannan mummunan lamari.
Hajiya Bahijja Kabara ta ce ba za a lamunci wasu bata-gari su riƙa kai wa ‘yan jarida hari ba, musamman a lokacin da suke gudanar da aikinsu ko kuma kan hanyarsu ta dawowa daga wuraren ɗaukar rahotanni.
Ta buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin da ya dace, tare da gudanar da bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan aika-aika da kuma hukunta su bisa doka.
Shugabar NAWOJ ta kuma yi kira ga shugabannin siyasa da su ja kunnen magoya bayansu, tare da tabbatar da cewa ba su kai wa ‘yan jarida hari ba yayin da suke gudanar da aikin ɗaukar rahotannin tarukan siyasa da gangamin yaƙin neman zaɓe, musamman a yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Kazalika, Hajiya Kabara ta buƙaci hukumomin tsaro a Jihar Kano da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu, domin hakan ya zama darasi ga sauran masu irin wannan ɗabi’a.
Da yake mayar da jawabi, Mukaddashin Shugaban Gidan Rediyon Najeriya Pyramid FM Kano, Malam Umar Nuhu, ya bayyana farin cikinsa, a madadin sauran shugabannin gidan rediyon, bisa ziyarar jajantawar da shugabannin NAWOJ suka kawo musu a matsayin abokan aiki.
Malam Umar Nuhu ya ce suna matuƙar godiya ga ƙungiyar, yana mai cewa irin wannan lamari ba zai karya musu gwiwa ba, illa ma zai ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da gudanar da aikin ɗaukar rahotannin harkokin siyasa da sauran ayyukan jama’a.
Ya ce ma’aikatan gidan rediyon za su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa, gaskiya da adalci, musamman yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.










