Kotun Majistare Mai Daraja ta Ɗaya da ke Kafin Maiyaki, Ƙaramar Hukumar Kiru a Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Chief Magistrate Muhammad Alhaji Isa, ta bayar da umarnin tsare wani matashi mai suna Nura, ɗan Hayin Gwarmai.
Ana zargin matashin da sauya sunan banki da lambobin asusun da aka bai wa wasu mutane, lamarin da ake zargin ya sa aka tura masa kuɗaɗe masu yawa. Rahotanni sun ce wani mai suna Rabiu ne ya ɗauke shi aiki a shago domin gudanar da harkokin POS.
Sai dai zargin ya kai ga kama Nura bayan jami’an ’yan sandan Ƙaramar Hukumar Kiru sun cafke shi. Mai gabatar da ƙara, Sajan Aminu Muhammad Ciromawa, ya gurfanar da shi a gaban kotu tare da gabatar da takardar tuhuma.
Bayan an karanta masa takardar tuhumar, wanda ake zargin ya musanta aikata laifin. Mai gabatar da ƙara ya kuma sanar da kotu cewa har yanzu ba a kammala bincike kan lamarin ba.
Bisa wannan dalili, Chief Magistrate Muhammad Alhaji Isa ya ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa 28 ga Satumba, 2026, tare da bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a hannun jami’an gidan ajiya da gyaran hali, ƙarƙashin Inspector Zakariya Abdullahi Kurawa.
Bayan fitowarsa daga kotu, wakilinmu Dantala Uba Nuhu Kura ya samu zantawa da wanda ake zargin, wanda ya bayyana halinsa cikin annashuwa.










