Wata Kotun Majistiri da ke garin Lafiya a jihar Nassarawa, ta bada izinin a liƙe takardar sammaci a Ƙofar Gidan Mawaƙin siyasa, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, sakamakon hana jami’in kotu miƙa masa takardar gayyata da masu tsaronsa su ka yi, kan zarginsa da neman tunzura al’umma da kuma tayar da tarzoma.
Wani mutum mai suna Muhammad Sani Zangina daga garin Mararraba ne ya shigar da ƙarar ta hannun lauyansa, Barista Muhammad Barde Abdullahi, inda yace zargin da ake yi wa Rararan da aikatawa, ya saba da doka ta 114 a Kundin Shari’a na penal code.
Rarara dai ya kira taron manema labarai ne a kwanakin baya, inda ya bayyana nadamar goyon bayansa ga tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, tare da zarginsa da wargaza kasar kafin mika ta ga Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu.
Yadda zaman Kotun Zaben Gwamnan Kano ta kasanta a Kotun daukaka kara











