DA DUMI-DUMINSU: Duk Kasar Da Muka Samu Tana Temakawa Iran Sai Ta Dandana Kudarta” a Cewar Donald trump
Trump Ya Yi Gargadi Ga Ƙasashen Da Ke Taimakawa Iran
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi gargaɗi cewa duk wata ƙasa da za ta ci gaba da taimaka wa Iran ta fuskar kuɗi, kasuwanci ko wasu hanyoyin tallafi za ta fuskanci mummunan hukuncin tattalin arziki.
Trump ya ce Amurka za ta ƙaddamar da wani gagarumin yaƙin tattalin arziki da ware Iran daga duniya, yana mai kiransa “Economic D-Day”. Ya kuma yi barazanar ɗaukar tsauraran matakai kan ƙasashe ko kamfanonin da za su bai wa Iran wata hanya ta ci gaba da samun kuɗaɗe ko kasuwanci.
Sai dai Trump bai bayyana takamaiman ƙasashen da za a hukunta ba, kuma bai fayyace irin matakan da za a ɗauka ba.
Rahotanni sun ce wannan mataki na zuwa ne yayin da rikicin Amurka da Iran ke ƙara tsananta, musamman kan batun Mashigar Hormuz da harkokin fitar da man fetur na Iran.










