Sabbin Hotuna Sun Nuna Yadda Na’urorin Kakkabe Makaman Sama Na Iran Suka Tarwatsa Manyan Jiragen Amurka Da Isra’ila
Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Iran sun ce Rundunar Kare Jiragen Sama ta IRGC Aerospace Force ta yi amfani da wani sabon tsarin kariyar sararin samaniya wajen harbo wasu jiragen yaƙi da jirage marasa matuƙa na Amurka da Isra’ila.
An wallafa hotunan tarkacen jiragen da suka haɗa da F-15E na Amurka, MQ-9 Reaper da wasu jirage marasa matuƙa, waɗanda Iran ta ce ta lalata a lokacin hare-haren.
Wannan na ƙara nuna yadda yaƙin sararin samaniya tsakanin Iran da Amurka/Isra’ila ke ƙara tsananta.









