Daga: Hassan Umar Gwammaja
Dan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar NDC a zaben shekarar 2027, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana Hon. Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin abokin takararsa.
An sanar da hakan ne a ranar Litinin bayan gabatar da Hon. Mustapha Kwankwaso a gaban kwamitin koli na jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki a wani taron da aka gudanar a Miller Road da ke Kano.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun dan takarar gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar, ya bayyana cewa zaben Hon. Mustapha Kwankwaso ya biyo bayan nazari mai zurfi da tuntuba da aka yi, domin karfafa manufar jam’iyyar, da hadin kan jam’iyyar NDC.
Sanarwar ta ce an zabi Hon. Mustapha Kwankwaso ne bayan tattaunawa da tuntuba da aka yi da bangarori daban-daban tare da yin la’akari da wasu fitattun mutane da suka cancanta.
Kotun Tarayya Ta Umarci INEC Ta Soke Rajistar ADC Da Wasu Jam’iyyu Hudu
Da yake magana kan wannan ci gaba, Kwamared Gwarzo ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa abokin takararsa zai taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manufofin gwamnatinsu idan suka samu nasara, yana mai cewa kwarewarsa, nagartar shugabanci da kuma karbuwarsa a tsakanin al’umma sun sanya shi zama babban jigo a wannan tikitin takara.
Hon. Mustapha Kwankwaso, wanda tsohon Kwamishinan Matasa da Wasanni ne na Jihar Kano, ya shahara wajen hidimtawa jama’a tare da bayar da gudunmawa a bangaren bunkasa matasa da ayyukan ci gaban al’umma.
Sanarwar ta kara da cewa jam’iyyar NDC ta yi imanin cewa hadakar Gwarzo da Kwankwaso na kunshe da kwarewa, gogewa, amana da jajircewar da ake bukata domin magance kalubalen da ke fuskantar Jihar Kano tare da samar da shugabanci nagari ga al’ummar jihar.
Mustapha dai shi ne Babban da ga jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabi Musa Kwankwaso .











