Masarutar Gaya ta sha alwashin Nada mutane da suke taimakawa talakawa da marayu da sauran Alumma a mukamai daban daban da suke masarautar domin yaba musu bisa Gudunmawar da suke bayarwa a yankunan.
Maimartaba Sarkin Gaya Alh.Dr.Aliyu Ibrahim ne ya bayyana haka a lokacin da yake Nada Alh.Safiyanu Galadima a matsayin Dallatun Gaya da kuma, Alh. Abdulkadir Galadima a matsayin Dangorubar Gaya da Alh.Ibrahim Gwadabe a matsayin Sarkin Tsaftar Gaya,Wanda ya gudana fadarsa dake garin Gaya.
Maimartaba Sarkin Gaya Dr. Aliyu yace,Nadin irin wadan nan mutane zai taimaka gaya wajen ciyar da Alumma gaba ta fannoni da dama.
Yace,makasudun Nada wadan nan mahimman mutane, a matsayin jagororin kowanne bangare shine,domin a kara musu kwarin gwiwa da karsashin ci gaba da taimakawa masu karamin karfi na wannan yankuna da kuma, sanyawa wasu sha,awar tallafawa masu bukata a kodayaushe.
Dr.Aliyu ya kara da cewa,Masarutar Gaya ba za ta gajiya ba,wajen zakulo irin wadanda suke jibuntar lamarin Alumma da taimakonsu a yayin da bukatar hakan ta taso.
Maimartaban ya yi kira a garesu da su kasance jagorori na gari da za su fara sanya al’amuran Alummarsu kan gaba wajen ganin sun magancesu.
A jabansu daban daban tun da farko,Sun godewa Maimartaba Sarkin Gaya, Alh. Dr. Aliyu Ibrahim Gaya,bisa zabarsu da ya yi a matsayin wadanda za su rike wadan nan mukamai na Shugabanni masu rike da masarautun Gargajiya.
Wadanda aka Nada akwai:Alh.Safiyanu Galadima a matsayin Dallatun Gaya, Sai Alh.Abdulkadir Galadima a matsayin Dangorubar Gaya da Alh. Ibrahim Gwadabe a matsayin Sarkin tsaftar Gaya,Inda kuma, Suka jaddada Aniyarsu na ci gaba da taimakawa Alumma da ciyar da Masarautar Gaya da ma Yankunan Karamar Hukumar Gaya dake nan jihar kano.
Ibrahim sani gama pyramid radio.











