Kungiyar masu Noman Alkama ta kasa Reshen jihar kano ta bayyana gamsuwarta da tsarin da Gwamnatin tarayya ta bijiro da shi domin fara kaddamar da Noman Alkama na kadada 70,000 a watan Nawamba mai zuwa a fadin kasar nan.
Shugaban Kungiyar masu Noman Alkama na kasa reshen jihar kano, Alh.Hashimu Abdullahi Rinji ne ya bayyana haka a lokacin da yake Zantawa da manema labarai a nan kano.
Hashimu Abdullahi yace, Kungiyar a shirye take wajen yin aiki kafada da kafada da Gwamnatoci a matakai daban daban wajen wayar da kan alumma mahimmanci Noman Alkama a lungu da sako na birni da karkara.
Kungiyar masu Noman Alkama ta kasa, tana da rijista da Gwamnatin tarayya da ta jiha da kuma,Kananan Hukumomin dake fadin kasar nan.
Shugaban yace, kasar Najeriya tana da fadi, Amma, wannan Kungiya ita ce wadda Gwamnatin ta Amince da ita a matsayin Kungiyar da take da kwafin komai a hannunta,kuma kungiyar ce da take da duk abubuwan da ake bukata na Shedar Cikakkiyar Kungiya.
Hashimu Abdullahi, yayi kira ga Alummar kasar nan da suke da Sha’awar shiga wannan Kungiya,da su zo domin kofa a bude take da zarar suna bukatar hakan.
Daga Karshe ya bukaci ‘Ya’yan Kungiyar masu Noman Alkama da su kasance masu hadin kan daya kamata wajen ciyar da Kungiyar gaba yadda ya kamata, inda yace, Kungiyar ta himmatu wajen yin duk maiyiyuwa domin kare muradan Kungiyar da ‘ya’yanta a kodayaushe.
Yace, Kungiyar masu Noman Alkama, Kungiya ce,da take son zaman Lafiya da kare martabar harkokin Noma Musamman Noman Alkama a koina cikin gida Najeriya da sauran kasashen ketare.
Ibrahim sani gama pyramid radio.












