Bayanai na nuni da cewa ma’aikatan ceto na can suna kokarin neman gawarwakin wadanda suka nutse a ruwan don a yi musu jana’iza.
Kwale-kwalen ya dauko mutane da aka kiyasta yawan su ya wuce mutum 50, mutanen sun fito ne daga jihar Neja zuwa cin kasuwa a garin Yauri na jihar Kebbi.
Wadanda suka ga yadda lamarin ya auko sun ce iska ne mai tsananin gaske ya taso, sai taguwar ruwa ta ja kwalekwalen daga nan sai ya nutse da mutane.
Shugaban karamar hukumar Yauri ta Jihar Kebbi Bala Muhammad Yauri yace kwale-kwalen ya dauko mutane da mutane da abinci kafin lamarin ya faru.












