Daga Hassan Umar Gwammaja
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta fitar da sanarwa dangane da zanga-zangar lumana da wasu tsofaffin jami’anta ke shirin gudanarwa a ranar Litinin, 21 ga Yuli, 2025, domin neman ’yancin su na fansho da kuma ficewa daga tsarin Contributory Pension Scheme (CPS).
A cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a madadin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, an bayyana cewa rundunar ba za ta hana wannan zanga-zangar ba, tunda doka ta ba da dama ga kowa ya bayyana ra’ayinsa cikin lumana.
Sai dai rundunar ta nuna damuwa da yadda wasu ke kokarin siyasantar da batun, tare da yada bayanan da ke da nufin bata suna da haifar da rudani. Rundunar ta jaddada cewa tun shekarar 2014 ana kokarin ganin an fice daga tsarin fanshon, amma matsalolin doka da na kasafin kudi ne ke hana hakan.
Rundunar ta ce tana kokarin samar da hanyoyi daban-daban domin rage wa tsofaffin jami’ai radadin rayuwa, ciki har da amfani da kudaden da take samu da kuma haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu domin ƙirƙirar sabbin shirye-shiryen tallafi.
Sufeto Janar na ’Yan Sanda ya umarci kwamishinonin ’yan sanda a fadin ƙasar da su tabbatar da an ba tsofaffin jami’an kariya yayin zanga-zangar, tare da hana duk wani yunkuri na tada hankali daga masu neman cin moriyar zanga-zangar.
Rundunar ta ce wannan zanga-zanga na da matukar muhimmanci, kuma ya zama dole a gudanar da ita cikin natsuwa da mutunta doka da kuma mutuncin rundunar. Ta kuma gargadi jami’an da ke aiki yanzu da kada su bari a jefa su cikin rikicin da zai haifar da matsala ga rundunar.
#Jaridarnagartacciya #kanopolice #BBCHAUSA #criminalcase #phonesnatching #FRSC #PoliceProtest #nogoingback #PSC #DSS #power #protest












