Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano ta sami Nasarar ciro Mutane biyu daga Rijiya
Mai magana da yawun rundunar ACFO Saminu Yusif Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun sami kira daga wani mutum mai suna Joseph Pitter daga unguwar Sabon Gari inda ya shaidawa hukumar tasu cewa wata mata Mai suna Maryam ta faɗa Rijiya inda ba su yi ƙasa a gwuiwa ba nan take suka garzaya gurin da lamarin ya faru suka yi nasarar fito da ita a raye Kuma suka Kaita asibiti .
Bayan Nan suka danka ta a hannun jami’in kwansabilari a rundunar yan sanda mai suna Mu’azu Abdullahi dake ofishin yan sanda na Sabon Gari.
Kazalika sun sami kira ta hanyar jami’in su mai suna SFS Sadi Gora daga Garin Gora dake karamar hukumar Madobi inda wani bawan Allah Mai larurar iskokai ya faɗa wata Rijiya kuma ya kasa fitowa.
Bayan sun sami kira ne suka garzaya domin kai masa ɗauki da taimakon Allah suka ciro shi suka garzaya da shi Asibiti daga bisani rai yai halinsa.










