• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Nigeria @63, Jawabin shugaba Tinibu

aksam by aksam
October 1, 2023
Reading Time: 5 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

JAWABIN MAI GIRMA, SHUGABA BOLA AHMED TINUBU, GCFR, SHUGABAN KASA KUMA BABBAN KWAMANDAN ASKARAWAN NAJERIYA A CIKAR JAMHURIYAR TARAYYAR NAJERIYA SHEKARU 63 DA SAMUN ‘YANCIN KAI, RANAR LAHADI 1 GA OKTOBA, 2023

‘Yan uwana ‘yan Najeriya,
Ina farin cikin yi muku jawabi a yau, ranar cikar kasarmu shekaru 63 da samun ‘yancin kai, a matsayina na shugaban kasarmu mai albarka, kuma dan uwanku dan Najeriya.

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

2. A wannan rana mai muhimmanci mai cike da fatan alheri, muna jinjina ga iyayenmu da suka kafa Najeriya, mazansu da matansu. Ba don su ba, da ba a samu kasar Najeriya ba. Gwagwarmayarsu, sadaukarwarsu, da jagorancinsu ne suka haifar da ‘yantacciyar kasar Najeriya mai mulkin kanta.

3. A wannan lokacin, muna karfafa wa juna gwiwar cewa a matsayinmu na ‘yan Najeriya, Allah ya yi mana baiwa a dunkule da kuma a daidaikunmu. Babu wanda ya fi wani a cikinmu. Nasarorin da Najeriya ta cimma su ne abin alfaharinmu. Kalubalen da muka jure wa su ne ke karfafar mu. Kuma babu wata kasa ko wani iko a duniya da zai iya dankwafe mu daga isa matsayin da ya dace da mu. Wannan kasar taku ce, ‘yan uwana. Ku so ta, ku karrama ta a matsayinta ta kasarku ta kanku.

4. Najeriya ta isa kasa a bar misali bisa yanayin zubi da tsarinta. Allah ya azurta mu da kabilu, addinai, da al’adu daban-daban. Sai dai dankon zumuncin dake tsakaninmu ya na da matukar karfi ko da yake ba ganin sa ake ba. Mun hadu kan buri guda daya na samar da zaman lafiya da cigaban al’umma, da fata guda na bunkasar arziki da hadin kai, da kuma manufofin hadaka na juriya da adalci.

5. Samar da kasa da aka dora bisa harsashin aiwatar da wadannan manufofi masu daraja kan al’ummomi mabanbata ya zamo aiki mai matukar albarka da yake fama da kalubale. Wadansu mutanen sun ce bai kamata a samu ‘yantacciyar kasar Najeriya ba. Wasu sun ce kasarmu za ta rushe. Har abada su na bisa kuskure. A nan, kasarmu ta kafu kuma a nan za ta tabbata.

6. A bana, mun tsallake wani siradi mai muhimmanci a tafarkinmu na tabbatar da cigaban Najeriya. Zaben da muka yi wa gwamnatin dimokradiyya ta bakwai a jere, na nuna cewa kasarmu ta yi riko da tsarin dimokradiyya da aiki da doka.

7. Ranar da na kama mulki, na dauki alkawurra kan yadda zan shugabanci wannan babbar kasa ta mu. Daga cikin alkawurran har da yi wa tattalin arzikinmu garanmbawul domin samar da tsaro ga rayuka, ‘yanci, da walwalar al’umma.

8. Na ce daukar tsauraran matakai ya zama wajibi domin dora kasarmu kan tafarkin walwala da bunkasar tattalin arziki. A ranar na sanar da kawo karshen tallafin man fetur.

9. Ina sane da wahalhalun da suka biyo baya. Idanuna suna gani kuma zuciyata ta na kunci. Ina son in bayyana muku dalilin da ya sa wajibi mu cigaba da daurewa a cikin wannan mawuyacin hali. Wadanda ke son a cigaba da tallafin man fetur da mummunan tsarin sauyin kudaden waje, mutane ne da ke son gina tafka-tafkan gidaje . Ni ba haka nake ba. Ni ba zan gina mana gida a bisa tubalin toka ba. Idan muna son gidanmu ya yi kwari, ya dade dole ne mu gina shi kan tsandauri.

10. Gyara abu ne mai ciwo, amma shi ne abin da ci gabanmu da daukakarmu ke bukata. A yanzu muna dauke da wahalhalun da za su kai mu zuwa ga makomar da za a raba arzikin kasarmu mai yalwa bisa adalci ga kowa da kowa maimakon wasu tsirarun mahandama su tattare a wurinsu. Zamu samar da Najeriyar da za a mayar da yunwa, fatara, da wahala su zama tsohon labari.

11. Ba na farin cikin ganin al’ummar kasar nan na fama da wahalar da ya kamata a ce an sauke ta a shekarun da suka wuce. Zan so a ce babu wadannan wahalhalun a yanzu. Amma dole ne mu daure idan muna son samun makoma ta gari.

12. Gwamnatina na yin bakin kokarinta wurin sassauta wannan wahala. Yanzu zan bayyana muku matakan da muke dauka domin rage wannan radadin da magidanta da iyalai ke fama da su.

13. Mun fara daukar matakan sauya tsarin tafiyar da gwamnati domin samar da daidaton tattalin arziki, yaki da hauhawar farashi, bunkasa ayyukan masana’antu, samar da tsaron rayuka da dukiya, da kuma tallafa wa talakawa da sauran mabukata.

14. Bisa tattaunawarmu da ‘yan kwadago, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, muna gabatar da karin albashi na farko inda za mu kara mafi karancin albashin gwamnatin tarayya ba tare da kara hauhawar farashi ba. A tsawon watanni shida masu zuwa, kananan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya za su samu karin Naira Dubu Ashirin da Biyar kowanne wata a albashinsu.

15. Domin kawo ci gaba a yankunan karkara, mun kafa asusun tallafi kan samar da kayayyakin more rayuwa domin jihohi su bunkasa bangarorin dake da muhimmanci a yankunansu. Tuni jihohi suka karbi kudi domin ba da tallafin sassauta radadin hauhawar farashin abinci da sauran bukatun yau da gobe.

16. Bunkasa tattalin arziki ta hanyar rage farashin sufuri na da matukar muhimmanci. Dangane da haka ne muka bude wani sabon babi a fannin sufuri ta hanyar samar da motocin haya masu amfani da iskar Gas a fadin kasar nan. Wadannan motoci za su caji kudi mai sauki da bai kama kafar yadda ake biya yanzu ba.

17. Ba da jimawa ba kayan aikin sauya motoci masu amfani da fetur zuwa gas za su fara isowa kasar nan saboda mun dauki matakan takaita lokacin da aka saba dauka kafin shigo da su. Kuma za mu kafa wurin bada horo a fadin kasa domin koyarwa da bada sababbin damarmaki ga masu harkar sufuri da kuma masu kafa masana’antu. Wannan lokaci ne mai muhimmanci da kasarmu ta rungumi hanya mafi inganci wurin samarwa tattalin arzikinmu makamashi. Samar da wannan sauyin, kafa sabon tarihi ne.

18. Na dauki alkawarin tsaftace barnar da ta yi wa Babban Bankin Kasa dabaibayi. Wannan aikin an riga an fara. An kafa sabon shugabanci a Babban Bankin. Kuma mai bincike na musamman da na nada na gab da gabatar da rahotonsa kan kurakuran da aka samu a baya da kuma hanyoyin da za a magance afkuwar hakan nan gaba. Daga yanzu, dokokinmu na tasarrufi da kudi za su amfani kowa da kowa ne maimakon masu iko da masu kudi kadai.

19. Dokar haraji mai hikima na da muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da adalci. Na kaddamar da kwamitin sauya fasalin tsarin haraji domin inganta tattara haraji a kasar nan da kuma magance dokoki marasa adalci ko masu kawo tarnaki ga ci gaban kasuwanci da bunkasar tattalin arziki.

20. Domin bunkasa samar da aikin yi da kudin shiga ga mazauna birane, mun samar da asusun zuba jari ga kamfanonin da suka nuna alamar makoma ta gari. Haka kuma mun kara zuba jari a kanana da matsakaitan kamfanoni.

21. Daga wannan watan, za a kara gidaje miliyan 15 kan wadanda ake bai wa tallafin kudi kai tsaye domin rage masu radadi.

22. Gwamnatina a ko da yaushe za ta ci gaba da bai wa tsaron al’umma muhimmancin gaske. Mun bunkasa hadin kai da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro. An dora wa manyan hafsoshin sojin muhimmin aikin farfado da karsashin rundunonimu.

23. A nan, nake jinjina da yabo ga dakarun tsaronmu, da suke ba mu kariya tare da tabbatar da tsaron kasarmu. Da yawansu sun riga mu gidan gaskiya. Muna tuna su a yau tare da iyalansu. Za mu bai wa dakarunmu kayan aikin da za su sauke nauyin da ke kansu a madadin al’ummarmu.

24. Zamu ci gaba da nada mutane bisa muhimman mukamai daidai da tanadin tsarin mulki na yin adalci ga kowa. Za a cigaba da kulawa da mata, matasa da masu bukatu na musamman a wadannan nade-naden.

25. Zan yi amfani da wannan dama domin taya Majalisun Dokoki na Kasa murna kan rawar da suka taka wurin kafuwar wannan gwamnati ba tare da bata lokaci ba ta hanyar gudanar da ayyukan da tsarin mulki ya dora musu na tantance wadanda za a nada da kuma sa ido kan yadda suke gudanar da ayyukansu.

26. Haka kuma ina taya bangaren Shari’a murna a matsayinsu na ginshikin dimokradiyya da adalci.

27. Ina kuma taya murna ga kungiyoyinmu na ci gaban al’umma da kungiyoyin kwadago bisa sadaukarwarsu ga dimokradiyyar Najeriya

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Yadda Yan kasuwar kayayyakin gona ke kokawa da farashin man fetur

Next Post

Yadda hukumar Makarantar shahada ta gabatar da shawarwari ga Dalibai

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan
LABARAI

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

by aksam
May 4, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano
LABARAI

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A  Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga  Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC
LABARAI

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC

by aksam
May 3, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Trump: Makomar Taiwan na Hannun Shugaban China Xi Jinping

Trump: Makomar Taiwan na Hannun Shugaban China Xi Jinping

January 9, 2026
Yadda zaman jaruman tiktok da hukumar Hisbah ya wakana a jihar Kano

Yadda zaman jaruman tiktok da hukumar Hisbah ya wakana a jihar Kano

November 7, 2023
ADVERTISEMENT

Trending.

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media