Aƙalla mutum 26 ne suka rasu sakamakon wasu sabbin hare-haren da aka kai wasu ƙauyuka a Jihar Binuwai.
Hare-haren sun faru ne a yankunan Ƙaramar Hukumar Makurdi da Katsina-Ala tsakanin ƙarfe 12 na dare zuwa 2 na daren ranar Alhamis.
’yan bindigar sun kai harin ne a ƙauyukan Mtswenem da Akondotyough Bawa, inda suka kashe mutum 25.
Haka kuma, an kashe mutum ɗaya a wani hari daban da aka kai ƙauyukan Kenvanger da Agbami a Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala.
Shedun gani da ido mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun shiga gidajen mutane suna harbin su yayin da suke barci, suna amfani da bindigogi da adduna.
Wani wanda ya tsira mai suna Iorpuu, ya ce mata da yara suna cikin waɗanda aka kashe, kuma har yanzu ana neman wasu da suka ɓace.
Ya ƙara da cewa wasu sun mutu ne a kan hanyarsu ta zuwa asibiti.
Wani ganau ya ce an fara kai harin ne wani ƙauye kusa da Jami’ar Noma da Fasaha ta Makurdi, inda aka kashe mutane huɗu.












