• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kasar China ta ba wa ƙasashe 47 damar shigar ta ba tare da visa ba

aksam by aksam
June 9, 2025
Reading Time: 1 min read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
469
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Tun daga yau Litinin tara ga watan Yuni, kasar China ta fara aiwatar da manufar bai wa ’yan wasu kasashe iznin shiga cikin kasar ba tare da takardar biza ba, ciki har da Saudiyya, da Oman, da Kuwait, da Bahrain.

Kawo yanzu, adadin kasashen da kasar Sin ta bai wa jama’arsu izinin shiga cikin kasar ba tare da takardar biza ba, ya habaka zuwa 47.

RelatedPosts

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Tun daga ranar 9 ga watan Yunin shekara ta 2025, zuwa ranar 8 ga watan Yunin shekara ta 2026, mutanen dake da takardar fasfo daga kasashen Saudiyya, da Oman, da Kuwait, da kuma Bahrain, idan suna so su shigo kasar Sin don yin kasuwanci, ko yawon bude ido, ko ziyartar iyalai da abokansu, ko kuma rangadin aiki na kasa da kwanaki 30, babu bukatar su nemi takardar biza na shiga cikin kasar wato “visa”.

Tuni a shekara ta 2018, kasar China ta aiwatar da irin wannan manufa ga Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Qatar, al’amarin da ya sa kawo yanzu kasar Sin ta aiwatar da wannan manufa ga dukkan kasashe membobin kungiyar GCC.

Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, karuwar yawan kasashen da kasar Sin ta bai wa jama’arsu izinin shiga cikin kasar ba tare da takardar biza ba, ya shaida babbar niyyarta ta fadada bude kofa ga kasashen waje, kana, Sin za ta ci gaba da kyautata manufofin shiga cikin kasar, da kara habaka yawan kasashen da manufar ta shafa, ta yadda baki ’yan kasashen waje za su kara jin dadin kayayyaki, da kasuwanni, gami da hidimomin da aka samar musu a kasar ta Sin, kuma kasashe daban-daban za su more ci gaba tare da kasar Sin bisa hadin-gwiwar da suke yi.

Share188Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Sojojin sun farmaki ‘ƴan ta’adda” a maɓoyarsu

Next Post

Shugaban kasar China ya gana da takwaransa na Koriya ta kudu

aksam

aksam

RelatedPosts

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala
LABARAI

Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala

by aksam
April 17, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID
Uncategorized

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

by aksam
April 17, 2026
Araqchi Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matsaya Ka
Uncategorized

Araqchi Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matsaya Ka

by aksam
April 11, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

NLC zata bukaci miliyan daya mafi karancin Albashi: Joe Ajaero

NLC zata bukaci miliyan daya mafi karancin Albashi: Joe Ajaero

February 12, 2024
Jawabin Tinubu ya ja hankalin shugabannin Africa su tausaya wa al’ummar su

Shugaba Bola Tinubu, Ya Amince Wa Kamfanin Man Fetur Na Ƙasa (NNPCL), Da Ya Yi Amfani Da Ribar Shekarar 2023 Da Aka Mamu Domin Biyan Tallafin Man Fetur.

August 19, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media