Daga Hassan Umar Gwammaja
Matashi dake zargi mai shekara 18 mai koyon sana’ar Dinke ya yi wa ƴan mata goma ciki a cikin watanni biyar a jihar Anambra, ciki har da ƴar ubangidansa da wata yarinyar shago.
A cewar rahoton The Punch, an tura matashin ne koyon sana’a karkashin wani ubangida. Sai dai cikin watanni uku da fara aikin, ya ɗirka wa ƴar ubangidansa da wata mai kula da shagon ciki.
Lamarin ya sa aka kori matashin daga wajen koyon sana’ar da ya ke.
Kwamishiniyar harkokin mata da walwalar jama’a ta jihar Anambra, Ify Obinabo, ita ce ta bayyana hakan a wani faifan bidiyo da aka yada kai tsaye a kafar sadarwa a ranar Laraba.
Bayan matashin ya koma kauyensu bayan wata biyu da korarsa, ya yi wa wasu ƴan mata takwas ciki, kamar yadda kwamishiniyar ta bayyana.
Ta ƙara da cewa mahaifiyar matashin ce da kanta ta kai ƙorafi ofishin ta dangane da abin da ɗanta ya aikata. Kwamishiniyar ba ta bayyana sunan matashin ba.










