RelatedPosts
- Daga Hassan Umar Gwammaja
Fadar Shugaban Najeriya, ta musanta labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ya ce Shugaba Tinubu ya sauke Ministocin kasar guda Uku.
Mashawarcin shugaban kasar kan yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce labarin ba shi da tushe ballantana makama.
Ministocin da aka ce an sauke sun hadar da na tsaro Muhammad Badaru Abubakar, da ministan kasa a ma’aikatar tsaron, Bello Matawalle da kuma ministan lantarki Adebayo Adelabu, adan haka Onanuga ya bukaci jama’a da su daina yarda da jita-jita mara tushe.
A cewar sa, “Wadanda ke yada irin wannan labari na bogi, masu laifi ne da ya kamata a hukunta su ba tare da bata lokaci ba, adan haka muna kira ga hukumomi da su dauki mataki kan irin wadannan kafafen dake yada labaran karya musamman wadanda za su tayar da hankalin al’umma”.












