Likitocin da ke lura da lafiyar fitaccen jarumin fina-finan Indiyan nan Saif Ali Khan da wasu ɓatagari su ka haura gidasa tare da caka masa wuƙa har sau shida a jiki sun tabbatar a yau cewa rayuwarsa ta fita daga cikin hatsari.
Jarumin wanda ke kwance a wani babban asibitin ƙasar mai suna “Lilavati Hospital” likitocin sun ce sun yi nasarar fitar da ɓallin wuƙar da maharan su ka caka wa jarumin a cikin lakarsa bayan sun yi mishi aiki.
Bayanai dai sun ce wannan lamari ya samu Ali Khan ne a lokacin da ya ke ƙoƙarin kare iyalinsa daga cutarwar ɓatagarin a daren ranar 16 ga watan Janairun wannan shekarar.











