Babbar kotun tarayya da ke zaune a jihar Lagos ta dakatar da Shirin hukumar kiyaye afkuwar hadura na kama ababan hawan da lambobin su suka kode.
Kana kotun ta ta ja kunnen hukumar da su guji yin Tara ko ladabtar da ko wanna direba da suka samu da kodaddiyar lamba a abin hawan SA.
Mai shari’a Aluko ya yi umarnin ne cikin hukuncin da ya yanke Mai lamba FHC/L/CS/253/2024, wanda Chinwike Chamberlain Ezebube suka kalubalanci hukumar FRSC a cikin SA.












