Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya cika ɗaya daga cikin alƙawuran da ya ɗauka yayin yaƙin neman zabensa, na bai wa ɗalibai rancen kudi don yin karatu.
Ma’aikatar ilimi ta ƙasa ce za ta gudanar da shirin lamunin, wanda ɗalibai marasa ƙarfi da suka yi rajista a manyan makarantu za su amfana
Dokar lamunin karatun ta kuma ƙunshi wasu hukunce-hukunce ga waɗanda suka gaza biya, kamar ɗauri da tara, don ƙarfafa biyan lamunin
Ma’aikatar ilimi ta ƙasa ce za ta gudanar da tsarin ba da kuɗaɗen lamunin, kuma ɗalibai marasa ƙarfi da suka yi rajista a manyan makarantun ƙasar nan ne kawai za su amfana da shirin.
Dele Alake, mai magana da yawun Shugaba Tinubu ya bayyana cewa babban maƙasudin ƙudirin shine samar da hanyar zuwa manyan makarantu ga ‘yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi ta hanyar asusun lamuni na ilimi na Najeriya.












