Daga Hassan Umar Gwammaja
Hakan ya fito ne ta bakin mai magana da yawun hukumar shige da fice ta kasa (NIS), DCI Kenneth Udo, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
A cewarsa, daidaita kudaden na daga cikin kokarin gwamnati na tabbatar da inganci da tsaron Passport din Najeriya.
Yanzu farashin “passport” da ake yi N35,000 mai shafuka 32 na tsawon shekaru 5 ya koma N50,000. Sai kuma “passport” mai shafuka 62 na shekaru 10, ya tashi N70,000, ya koma N100,000.









