Daga: Hassan Umar Gwammaja
Fastocin sun nuna cewa Ganduje wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na kasa a yanzu, zai tsaya takarar shugaban kasa, yayin da Uzodinma wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC, zai kasance mataimakinsa.
Fastocin da ke dauke da taken, ‘Ga ‘Yan Najeriya, wadata da ci gaban bil’adama’ sun kuma nuna cewa ‘yan siyasar biyu za su fafata a zaben 2027 a karkashin jam’iyyar APC.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙura ta taso kan yunkurin tsige Ganduje daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar APC na kasa domin neman mukamin jakadanci, ikirarin da kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na kasa (NWC) ya bankado a matsayin karya.
Sai dai kuma da ya ke mayar da martani, Ganduje ya bayyana fastocin a matsayin aikin ‘yan hamayya
Edwin Olofu, Babban Sakataren Yada Labarai na Ganduje, a wata tattaunawa ta wayar tarho da Daily Trust ya ce, “Abin dariya ne kuma yarinta ne, kuma aiki ne kawai na ‘yan hamayya.











