Daga Hassan Umar Gwammaja
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jagorancin taron majalisar koli ta farko tun bayan hawansa karagar mulki.
Daga cikin mahalarta taron harda tsoffin shugabannin kasar da suka hada da Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan da Yakubu Gowon da kuma Abdusalami Abubakar.
Sai dai an ruwaito cewar Olusegun Obasanjo bai samu damar halartar taron ba.
Ita dai wannan majalisa ta bai wa shugaban kasa shawara ta kunshi tsoffin shugabannin kasa da shugabanin majalisun dokoki masu ci da wadanda suka shude da alkalin alkai mai ci da wadanda suka yi ritaya.
Majalisar kan tattauna wasu manyan batutuwa da suka shafi kasa domin bai wa shugaban kasa mai ci shawara a kan yadda zai tinkare su.
Ana saran shugabannin su tattauna batun zanga-zangar da matasa suka yi da tsadar rayuwar da jama’a ke fuskanta da kuma halin da kasa ke ciki.










