Daga Hassan Umar Gwammaja
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da nadin wasu kwararrun ‘yan Najeriya bakwai da za su shugabanci wasu hukumomi dake karkashin ma’aikatar jin kai, kau da bala’o’i da ci gaban al’umma ta tarayya.
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da:
1 – Badamasi Lawal zai kula da hukumar NSIPA, Badamasi Lawal ɗan asalin jihar Katsina ne.
2 – Funmilola Olotu za ta kula da ma’aikatar NSSCO
3 – Aishat Alubankudi – Za ta kula da bangaren kula da mutane masu rauni, a matsayin babbar manaja.
4 – Aderemi Adebowale – Za ta kula da sashen ciyar da ɗalibai abinci a makaratu
5 – Abdullahi Alhassan Imam – Manajan Shirye-Shirye, Ofishin raba Kudi na Kasa
6 – Ayuba Gufwan – Babban Sakatare, Hukumar Kula da Nakasassu ta Kasa
7 – Lami Binta Adamu Bello – Darakta Janar na Hukumar Hana Fatauci da safarar mutane ta kasa












