Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa Sanata Shehu Sani ya ce lokaci ya yi da ’yan Arewa za su zargi kansu akan matsalolin da yankin ke fama da shi maimakon zargin wasu yankuna ko shuwagabanni.
Sani wanda ya rubuta a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi ya koka da cewa yawancin makarantun Gwamnati a yankin kyauta ne amma har yanzu matasanmu ba sa son zuwa Makaranta.
Ya ce “Da yawa daga cikinmu ba sa son Matan su yi aiki ko kuma su yi amfani da basirarsu ko hikima don samun abin dogaro da kai ko kuma ba da gudummawar iyali, shiyasa idan muka mutu mukan bar su a matsayin zawarawa marasa abin yi cikin tausayi da neman ɗauki.
Yawancin Matasa ba sa son yin aiki a matsayin masu koyo ko yara a wuraren koyon sana’o’i ko wuraren sayar da kayayyaki saboda ba su da zuciya da haƙurin juriya wajen neman dukiya ta halal.
Iyaye da dama a yankunan karkara suna miƙa ’ya’yansu ga Malaman addini a cikin birane wanda kuma mafi yawa sukan dogara ne da yaran su yi bara ko sata don ciyar da kansa da baiwa iyayen sa. Bisa dalilai na kabilanci, mun kare, mun yaba kuma mun ƙi bin diddigin jagororin kasar nan da suka fito daga yankin a duk wata damar da aka bata tsawon shekaru hamsin.
‘Yan fashi da ’yan ta’adda da suke kashe jama’a da garkuwa da su, suna hana manoman mu noma a gonakinsu, suna hana ‘ya’yanmu zuwa Makaranta, ba daga wata ƙasa suke ba ko kuma daga yankin Kudu, sun fito daga gidajenmu da iyalanmu a Arewa.
Muna ibada da su a masallaci guda, Mun kasance tare a matsayin yanki ɗaya cikin aminci da ‘yan’uwantaka da soyayya, amma sai muka rabu muka fara kyamar kanmu ta bambancin fahimtar addini.
Ba ma zabar Mutanen da za su yi mana hidima; muna zabar Shugabanni ne waɗanda za su samar mana da Taliya da hatsi.
Mun shirya tare da yada duk wani makirci na addini don hana yaranmu rigakafin lafiya kyauta daga cututtuka wanda ka iya haifar da dubban daruruwan makafi, da guragu, da kurame da suka tashi a matsayin masu fama da cutar polio, ko glaucoma, ko kuturta suna barace-barace a garuruwan Arewa da kudu. Yawancin yaranmu Mata ba su da jarin kasuwanci na dubu 100, amma sun mallaki wayar iPhone wadda ta kai darajar Naira Miliyan 1.5, za ka samu
Ba su da jari na dubu 100 amma suna iya yin fafutuka don mallakar atamfar biki ta Naira dubu 50.
Mun hana yawancin ƴaƴanmu Mata damar wucewa Makarantar gaba da Sakandare saboda munanan hasashe game da manyan makarantun, Ba ma son yaranmu mata suyi aikin sanya Unifom, a duk lokacin da aka bude kofofin daukar ma’aikata a Hukumar Shige da Fice, da ta Rundunar ƴan Sanda, da Civil Defence ba za mu so su nema ba.
Lokacin da ‘ya’yanmu suka kammala karatu a jami’o’i Musamman jami’o’in Gwamnati galibin iyayen da suke zuwa bikin yaye ɗalibai da kuma yaba ƙwazon ‘ya’yansu iyaye ne daga yankunan Kudu, Yawancin kamfanonin mu na Kano, da Kaduna, da Jos an rufe su tun lokacin da ‘yan yankinmu ke kan mulki. Manoman mu na karkara har yanzu suna noma da fartanya a tsawon lokacin da ’yan yankin namu suka yi mulki. Noman Gyada da auduga duk sun ɓace tuntuni a yankunan namu.
Dukkanin kayayyakin gine-gine da shagunan sayar da magunguna da ke arewacin kasar, sana’o’i ne masu zaman kansu na mutanen da suka zo daga wasu yankuna, waɗanda ba wata Gwamnati bace ta tallafa musu da kasuwancin ba, A lokacin da ’yan yankinmu suka yi Mulki mun danganta talauci da rashin tsaro ga Allah da zunuban da muke aikatawa, amma yanzu sai mu danganta hakan da Shugabanni.
Abuja tana yankin Arewa ne, Shin akwai wanda zai iya bayyana dalilin da ya sa mutanen yankin suka kasa mamaye harkokin kasuwanci masu zaman kansu a Abuja, da Suleja, da Mararaba? To yanzu wa ya kamata a zarga da wannan?
“Allah ya bamu mafi girman ƙasa mafi yawan jama’a, mafi yawan yankuna da ke da albarkatu da dabbobi kuma ya bamu iko a tarihin mu.
Wanne daga cikin ni’imomin Ubangijinmu za mu iya musun cewa muna dashi a Arewa?
kashi 80 cikin 100 na matsalolinmu laifin mu ne da kanmu ba wani ba”.











