Daga Sadiya Yakubu Lawan
Tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya nesanta kansa da wani rubutu da aka danganta shi da shi
Janar IBB ya ce ko kaɗan rubutun wanda aka yi a shafin X mai cewa ya fi son mulkin soja a ƙasar nan fiye da na dimokuraɗiyya, ba daga gare shi ba ne
Tsohon shugaban ƙasan na Najeriya ya koka kan yadda shafin ya daɗe yana yaɗa kalaman ƙarya da sunansa
Shafin mai suna @General_Ibbro a manhajar X (wacce a baya aka fi sani da Twitter), ya ce Ibrahim Badamasi Babangida ya fi son mulkin soja fiye da na dimokuraɗiyya, cewar rahoton tashar Channels tv.











