Sabon Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya Koka da yadda tsohon gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje ya bar masa bashin da yakai sama da Naira Biliyan 241 .
” Wanann abun da tsohuwar gwamnati ta yi mana abun takaici ne na bar masa bashin da yakai Sama da Naira Biliyan 241, a Ina za mu samu wadannan kudaden har mu biya”. Inji Abba gida-gida.
Sabon gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya karɓi ragamar mulkin jihar Kano a Gidan gwamnatin Kano.
Abba Kabir Yusuf ya bada tabbacin zai duba yadda gwamnatin da ta gabata ta gudanar da mulkin da kuma daukar matakan da suka dace.
” Na zaci tsohon gwamna Ganduje zai tsaya da kansa ya mika mulki kamar yadda aka Saba a nan kano, a Shekarar 1999 Kwankwaso ya mika mulki ga Kwankwaso, Kwankwaso kuma ya mika mulki ga Shekarau a 2003 , haka kuma Shekarau ya mikawa Kwankwaso mulki a Shekarar 2011, shi ma Kwankwaso ya mikawa Ganduje Kwankwaso mulkin a Shekarar 2015 , amma kuma ni Mai yasa ba zai tsaya ya mikamin mulki ba sai dai ya sa wakili ? “. Inji Abba Gida-gida
Engr. Abba Kabir Yusuf ya baiwa al’ummar jihar kano tabbacin gwamnatin sa zata yi duk mai yiyuwa wajen ganin bai basu Kunya












