Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a babban zaben da ya gudana a shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar, da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo, ba su cire rai da samun nasara a Kotu ba.
Atiku da Namadi Sambo sun roki mambobin jam’iyyar su ta PDP da su dunƙule wuri guda kuma karsu cire rai da samun nasarar jam’iyyar a Kotun sauraron karar zaben shugaban ƙasa.
- Namadi Sambo ya koka da yadda ake kara samun rikici-rikice tsakanin ‘ya’yan jam’iyar ta PDP musamman a matakin jihohi











