• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Dalilan SERAP na neman cikakken bayanin biliyan 100 daga gwamnan CBN

aksam by aksam
June 30, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
468
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta buƙaci gwamnan babban bankin ƙasar, Mista Olayemi Cardoso ya yi bayani kan ”yadda fiye da naira biliyan 100 na takardun kuɗin da suka lalace – da sauran kuɗi masu yawa da ke jiran tantancewa a rassan CBN ɗin – suka yi ɓatan dabo.

Cikin wata wasiƙa da ƙungiyar ta wallafa a shafnta na intanet, ta ce ta samu zarge-zargen ne cikin rahoton shekara-shekara da babban mai binciken kuɗi na ƙasa ya fitar a 2022.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

“Rahoton babban mai binciken kuɗin na 2022 ya nuna cewa, tun a 2017 CBN ke ci gaba da taskance fiye da naira biliyan 100 na takardun kuɗin da suka lalace ko suka yi dauɗa, da wasu kuɗi masu yawa da ke jiran tantancewa a rassan CBN”.

Rahoton babban mai binciken kuɗin na fargabar cewa an karkatar, ko an sake maido da ”lalatattun takardun kuɗin da kuɗaɗen masu datti” da aka tsara cewa za a ƙone su.

Ƙungiyar ta ce zarge-zargen da ke cikin rahoton babban mai binciken kuɗin ya nuna yadda CBn din ya saɓa wa kundin tsarin mulki da dokar CBN da dokokin cin hanci na ƙasa da ma na duniya.

Haka kuma ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnan na CBN ya yi ƙarin haske ”kan inda naira biliyan 7.2 da aka ware domin gina resehn bankin a Dutse a shekarar 2010, da kuma naira biliyan 4.8 da aka ware don sabunta resehn CBN na birnin Abeokuta a shekarar 2009.

Serap ɗin ta kuma buƙaci CBN din ya wallafa sunayen ‘yan kwangilar da aka bai wa ayyukan, kuma suka gaza aiwatar da su.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci CBN din ya yi wa jama’a bayani kan wasu basuka da bankin ya bai wa wasu jihohin ƙasar.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Sema ta fitar da sabon adadin wadanda suka mutu a harin Gwoza

Next Post

Kungiyar Mata Masu Koyar Da Sana’o’in Hannu Domin Dogaro Da Kai Dake Jihar Kaduna (EDAK), Ta Yaye Dalibain 150 Da Ta Koya Sana’o’i Daban-Daban

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

September 1, 2026
An Samu Gagarumin Ci Gaba a Aikin Gadar Sama ta Tal’udu a Kano

An Samu Gagarumin Ci Gaba a Aikin Gadar Sama ta Tal’udu a Kano

April 30, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media