DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
Burkina Faso ta sake dakatar da wasu kafafen yada labarai daga yada shirye-shiryensu a kasar, sakamakon fitar da rahoton hukumar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch, da ta zargi sojojin kasar da yi wa wasu mutanen karkara fararen hula 223 kisan gilla.
DW ta ruwaito cewa Kafafen yada labaran da dakatarwar ta yanzu ta shafa sun hada da Deutsche Welle da ke nan Jamus, da jaridar Faransa ta Le Monde, da Quest-France, sai jaridar Guardian ta Burtaniya da kamfanonin dillancin Afirka na APA da kuma Ecofin.
Channelstv ta ruwaito cewa Burkina ta fara dakatar da BBC da VOA, da kuma gidan talabijin din Faransa na TV5Monde.
Rahoton na Human Rights Watch ya zargi sojojin Burkina Faso da hallaka fafaren hular 223 a cikin watan Fabarairun da ya gabata, bisa zarginsu da hada baki da ‘yan ta’adda











