Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal ya soki yadda Shugaban kasa Bola Ahmed Tinibu ya soke tsarin bayar da tallafin man fetur.
A wata zantawa da The Cable tayi da shi, Babachir David Lawal ya zargi Bola Ahmed Tinubu da gadara wajen cire tallafin man fetur
Dan siyasar yake cewa garaje da sabon shugaban Najeriyan ya yi ranar da aka rantsar da shi ya jefa Najeriya a cikin kuncin rayuwa.
Tsohon jagoran na APC mai mulki ya zargi Bola Ahmed Tinubu da nuna rashin imani da girman kai tun wajen dauko abokin takaransa.
Babachir yana ganin bai dace a matsayinsa na musulmi, Tinubu ya dauko musulmi ba,
bayan nan kuma sai ya jawo fetur ya kara tsada. Zancen Babachir David Lawal
“Ra’ayina shi ne girman kai ya tunzura aka cire tallafin fetur.
An rantsar da kai kuma kana son nuna kai ne a kan karagar mulki yanzu, Za ka iya danne kowa, sai kurum ka sanar da cire tallafi ba tare da tuntubar kowa ba.”












